1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotun Masar ta daure tsohon shugaba Morsi

Suleiman BabayoApril 21, 2015

Kotun kasar Masar ta yanke wa tsohon shugaban kasar Mohamed Morsi hukuncin shekaru 20 a gidan yari bayan da ta sameshi da laifin da ake zarginsa da aikatawa.

https://p.dw.com/p/1FBjL
Mohamed Mursi Urteil Kairo
Hoto: Reuters/Abdallah Dalsh

Wata kotun kasar Masar ta daure hambararren Shugaban kasar Mohamed Mursi na tsawon shekaru 20 a gidan fursuna, saboda musguna wa masu zanga-zanga amma an wankeshi daga laifukan da zai fuskanci hukuncin kisa.

A shari'a na farko kan tuhume-tuhumen da yake fuskanta kotun ta samu Mursi da laifin ba da umurnin cin zarafin masu zanga-zanga.

Mohamed Mursi ya zaben zaben demokaradiyya na farko a kasar ta Masar wanda ya gudana a watan Mayu na shekara ta 2012, amma gwamnatinsa ta kawo karshe a tsakiyar shekara ta 2013, bisa rarrabuwa da aka samu tsakanin al'umar kasar.