1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu ta aike da tsohon gwamnan jihar Jigawa kurkuku

Nasir Salisu Zango/ MNAJuly 9, 2015

Babbar kotun tarayya a Kano ta ce tsohon gwamnan na Jigawa Alhaji Sule Lamido ya zauna kurkuku har zuwa 28 ga watan Satumba.

https://p.dw.com/p/1Fvn9
Porträt - Sule Lamido
Hoto: Getty Images

Babbar kotun tarayya da ke zama a Kano Karkashin mai shari'a justice Evelyn Anyadige, ta aike da tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido kurkuku har zuwa ranar 28 ga watan Satumba.

Wannan mataki ya biyo bayan tuhumar da hukumar EFCC ke wa gwamnan tare da yayansa biyu Aminu Sule Lamido da Mustapha Sule Lamido.

Kotun dai ta ki amincewa da neman belin wadanda ake tuhuma a zaman na wannan Alhamis, amma tace akwai damar zuwa Kotun a Abuja domin neman beli kasancewar ita mai shari'ar za ta tafi hutu ne daga ranar Jumma'a.

Sai dai lauyan Sule Lamido Barista Offiong Offion SAN, ya soki lamirin matakin kotun yana mai cewar an keta hakkin wadanda yake karewa kamar yadda kundin tsarin mulkin Nigeriya ya basu.