1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotun Tarayyar Turai ta cire Hamas daga jerin kungiyoyin 'yan ta'adda

Mohammad Nasiru AwalDecember 17, 2014

A wannan Laraba ce babbar kotun Kungiyar EU ta ce ba a bi hanyoyin shari'a kwarara ba wajen sanya sunan Hamas a jerin kungiyoyin 'yan ta'adda a shekarar 2001.

https://p.dw.com/p/1E6F1
Luxemburg Europäischer Gerichtshof EuGH Schild
Hoto: picture-alliance/dpa/T. Frey

Kungiyar Hamas da ke jan ragamar mulki a Zirin Gaza a wannan Laraba ta yaba da hukuncin da wata kotun Tarayyar Turai ta yanke inda ta ba da umarnin cire sunan kungiyar daga jerin sunayen kungiyoyin 'yan ta'adda. Kakakin Hamas Fawzi Barhum ya fada wa kamfanin dillancin labarun AFP cewa matakin nasara ce ga batun Falasdinawa da kuma 'yancin al'umarsu. A wannan Laraba ce babbar kotun Kungiyar EU ta ce ba a bi hanyoyin shari'a kwarara ba wajen sanya sunan Hamas a jerin kungiyoyin 'yan ta'adda a shekarar 2001. Ta ce a lokaci an dogara a kan rahotanni daga kafafan yada labaru da kuma intanet. A martanin da ya mayar Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya bukaci EU da nan-take ta sake mayar da suna Hamas a jerin 'yan ta'adda. Duk da wannan hukuncin dai Kungiyar EU ta ce har yanzu a gareta Hamas kungiya ce ta 'yan tarzoma.