1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotun Togo ta halarta takarar Gnassingbe

Mouhamadou Awal BalarabeMarch 12, 2015

Shugaban Faure Gnassingbe na Togo ya samu damar yin tazarce bayan da kotun tsarin mulkin kasarsa ta sanya sunansa a cikin jerin wadanda suka cika sharudan shiga zabe.

https://p.dw.com/p/1Eq2h
Hoto: Reuters/Noel Kokou Tadegnon

Kotun tsarin mulkin kasar Togo ta amince shugaban mai ci a yanzu Faure Gnassingbe ya sake tsayawa takara a karo na uku a zaben da zai gudana a wata Afirilu mai zuwa, duk kuma da adawa da wani bangare na siyasa ke nunawa. Da ma dai tun bayan da aka kwaswkware kundin tsarin mulkin Togo a shekara ta 2002, doka ta cire shinge da ke kayaade yawan wa'adin da shugaban ya kamata ya yi a kan karagar mulki.

'yan adawa da kuma shugabannin fararen hula sun ta fantsama a kan tituna da nufin taka wa shugaban Gnassingbe birki a kokarin da ya ke yi na yin tazarce. Shi dai Faure wanda ya yi karatu a kasashen Faransa da kuma Amirka ya dare kan kujerar mulki ne a shekara ta 2005 bayan rasuwar mahaifinsa Eyadema wanda ya shafe shekaru 38 a kan kujerar mulki.

Su ma dai daukacin 'yan adawa ciki har da madugunsu Jean Pierre Fabre sun samu amincewar kotun tsarin mulki wajen tsayawa takara a zaben shugaban kasa.