1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koyon Jamusanci a Kamaru

November 20, 2013

'Yan kasar Kamaru da dama na kara nuna sha'awar magana da harshen Jamusanci duk da cewa suna amfani da harsunan Faransanci da Ingilishi

https://p.dw.com/p/1ALNx
DW-Tage am Goethe Institut Addis Abeba, Äthiopien, alle Fotos: Reategui Die Themen: Sprache, Radio und Sprache, Sprachpolitik in Afrika, Die DW in Äthiopien, Vorstellung des Deutschkurses in Amharisch, Koproduktion mit Radio Ethiopia zum Thema Schuldenerlass, zweiwöchiger Ausbildungskurs des DWFZ für Radiojournalisten und -techniker

Baya ga makarantu da ke koyar da harshen a matsayin kwasa-kwasan da ake yi, harshen Jamusancin ma ya kasance darasi a wannan kasa da ke Afrika ta yamma wacce tuni take amfani da harsunan Turanci da Farasanci a mastayin harsuna na kasa.

A cibiyar raya al'adun kasar Jamus ta Goethe da ke Yaounde dalibai dubu biyu ne suka yi rijista domin koyon harshen Jamusanci a cikin wannan shekara. Wasu daga cikin daliban sun ce suna sha'awar koyon harshen ne, saboda suna so yin karatu a Jamus. Sun bayyana cewa ingancin karatun da ake yi a Jamus na daga cikin wadanda suka fi kowane kyawo a duniya.

Daya daga cikin daliban Monika Kamsi, tace danuwanta wanda ya yi karatu a jami'ar Tubinguen shine ya kara mata kwarin guiwa ta koyi harshen Jamusancin. To ko ta yaya take fuskantar koyon harshen jamusanci

''Tace abu ne mai kyau domin wasu kalmomin sun yi kama da na turanci, saboda haka ina fahimta sosai cikin hanzari''.

Wani dalibin daban kuma mai suna Alfred Kautche wanda ya wo tafiyar kilomita 300 daga birnin Duala domin ya koyi harshen Jamusanci ya bayyana cewa.

Die Künstler Pascale Marthine Tayou (l) mit dem Künstler-Duo Salifou Lindou (m) und Hako Hankson (r) vor deren Atelier in Douala, Kamerun. August 2011 (Foto: DW / Aya Bach)
Shirin koyon sarrafa abubuwaHoto: DW / Aya Bach

Ra'ayoyin ɗaliban makarantar

Na yanke shawarar in koyi harshen Jamusanci ne saboda in kara zurfafa karatuna a kasar Jamus. Kuma ina da 'yan uwana a can don haka zai zama abu mai sauki in zama dan gari.

Mafi yawan malamai a cibiyar raya harshen Jamusanci ta Goethe da ke Kamaru 'yan asalin kasar ne. Michel Mokwelle na daya daga cikinsu wanda ya bayyana inda ya koyi harshen Jamusanci.

''A lokacin da danuwana ke koyon harshen Jamusanci yakan zo da wasu kyaututtukan da malamai kan bashi, don haka na ce zan koyi harshen jamusanci in ma fi shi''.

Ba a cibiyar raya al'adun kasar jamus ne kadai ake koyar da harshen Jamusanci a kasar Kamaru ba. Ana ma koyar da harshen a matsayin darasi a makarantun sakandire. Akwai sashi na koyar da harshen Jamusanci a jami'ar Yaounde, a bana dalibai dubu daya ne suka yi rijista domin koyon harshen. Sule Saidu malami ne kuma kwararre a fanin harsuna; yace mafi yawan 'yan kasar Kamaru suna koyon Jamusanci ne bisa dalilalai na tattalin arziki.

''Ai inda tattalin arziki yake da kyawo nan ne jama'a suka fi zuwa. Jamus ce kasar da tafi karfin tattalin arziki a nahiyar turai, kuma in har kana son hulda da wannan kasa to ya zama wajibi ka kware a harshen Jamusanci''.

Neu Delhi (Indien): Aufmerksam lesen indische Studenten am 05.03.2003 im deutschen Goethe-Institut in der indischen Hauptstadt Neu-Delhi in der Bibliothek. Hunderte Inder nutzen die Veranstaltungsangebote und die Bibliothek des "Max Müller Hauses", unter dem das Institut in Indien bekannt ist. Max Müller (1823-1900) ist in Indien der bekannteste deutsche Indologe. (BRL473-070303)
Ɗaliban makarantaHoto: picture-alliance/ ZB

Sakamakon bincike

Alkaluman lissafi daga ofishin jakadancin kasar Jamus da ke Yaounde sun nuna cewar kusan dalibai 'yan Kamaru dubu biyu ne ke samun takardar bisa ta izinin shiga kasar Jamus domin karatu a kasar da al'ummarta basu wuce milyan 20 ba in aka kwatanta da Najeriya da ke da dalibai 500. Jakadan kasar Jamsu a Kamaru Klaus-Ludwig Keferstein yace wannan na faruwa ne saboda yawan 'yan Kamaru da ke jin harshen Jamusanci.

''Suna da hazaka sosai kuma suna nuna hakan. Muna da 'yan kasar Kamaru kusan dubu shida da ke karatu a Jamus kuma idan ka kwatanta da da sauran kasashen da ke yankin Saharan Afarika sune suka fi yawa, mabi da su sune 'yan Najeriza wadanda suka kai 500''.

Kasar Kamaru dai tana da danganta mai tarihi da kasar Jamus, domin kuwa Jamus ta taba yiwa Kamaru mulkin mulkin malaka. Jamus ta bar gine-gine na mulki masu yawa wadanda ke da inganci. Wannan yasa wasu na cewa ai da Jamusanci ne ma ya zama harshen gwamnatin kasar Kamaru baya ga harsunan Turanci da Faransanci.

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris

Edita: Saleh Umar Saleh