1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarihin Zabi Sonka a DW Hausa

Yusuf BalaFebruary 9, 2016

A da can ana karbar sakonni na masu saurare ne ta gidajen waya inda suke turo da katin gaishe-gaishe.

https://p.dw.com/p/1Hrzo
50 Jahre Haussa Redaktion
Murjanatu Katsina a tsakiyar ma'aikatan sashin Hausa a shekarar 1972Hoto: DW

Mahadi mai dogon zamani na sashin Hausa na DW wato Umaru Aliyu, wanda ya kwashe sama da shekaru arba'in a wannan sashi, ya bada amsar wannan tambaya.

To shi shirin Zabi Sonka shiri ne da ya dauki lokaci me tsawo ana yinsa a wannan gidan rediyo wanda kusan za a iya cewa yana daya daga cikin shirye-shirye da aka bude sashin Hausa da su wato sama da shekaru 40 zuwa 45 kenan ni kaina na zo na tarar da shirin ne a na yinsa a wannan sashi. Kuma wannan shiri ya kasance daya daga cikin shirye-shirye masu farin jini da wannan sashi yake alfahari da su.

Wadanda suka bude sashin na Hausa na DW a wancan lokaci sun fahimci cewa shirin na da farin jini kuma idan suna so su tafi da masu saurare ya kamata su rika gabatar da shi, kuma shirin ba wani abu ya kunsa ba sai gaishe-gaishe na sada zumunci tsakanin masu saurare ko 'yan uwa da abokan arziki. Abin da dan Zabi Sonka ke so shi ne a bayyana sunansa a rediyo sannan ya yi amfani da wannan dama ya sada zumunta.

To ko a wancan lokaci, baya ga masu saurare ko ku ma masu aiki a wannan shashi kuna mu'amala da masu sauraren?

Kwarai kuwa domin zaka ga ko yanzu ake gabatar da wani shiri kana jin sunan wasu ka san tsaffin 'yan zabe ne. Wasu muna mu'ammala da su kai tsaye mun sansu, sun sanmu wasu kuwa muna sada zumanta ne ba kai tsaye ba.

Umaru Aliyu
Umaru Aliyu na sashin Hausa na DWHoto: DW/T. Mösch

To a wancan lokaci ta yaya wannan gidan rediyo ke karbar sakonni na masu saurare?

A wancan lokaci muna karbar sakonni ne ta akwatin gidan waya sai kaga an turo da katin zabe da yawa , mutum guda sai ya turo da kati goma ko ma fiye da haka, abin da ya sanya zaka ga an karanta masa ko da daya ne kuwa, lokacin babu wasu hanyoyin sadarwa, muna karba ne ta akwatin gidan waya daga baya ma muka rika karbar kaset da muryoyi na masu saurare ko da yake wannan na da dan wahala yadda ake juya muryar daga kaset zuwa na'urorin da muke da su, dan haka wannan tsari bai yi nisa ba, sannan kaset din kafin yazo yana iya daukar lokaci . A lokacin bayan a garuruwanmu zaka ga akwai mai buga katin zabe, mutane na zuwa wurin dan a buga musu su sada zumunta. Amma yanzu muna karbar sakonni ta hanyoyi na zamani kamar su e-mail da Facebook da dai sauransu. Sannan ga shi muna daukar muryoyi ta wayar tarho kamar ranar Laraba wacce a ranar ne ake tsara shirin. Koda yake ana iya dauka wani lokacin, ba a ranar Asabar ko Lahadin ake dauka ba, a ranar watsa shirin ake yi kawai.

Mutanen da suka jagoranci shirin a baya

Daya daga cikin matan da suka jagoranci shirin ita ce Murjanatu Katsina da Wasilatun Tanko wacce ni kaina na tarar tana gabatar da shirin, amma dai ina ga Murjanatu Katsina ita ce ta farko da ta jagoranci shirin na Zabi Sonka, kafin daga bisani wasu su biyo baya har zuwa wannan lokaci.