1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kudancin kasar Sudan na ci gaba da fuskantar hare-hare

Zulaiha Abubakar
April 23, 2018

Wani rahoto da cibiyar bincike kan yara kanana da rikici dake kasar Amirka ya fitar ya bayyana cewar akalla asibitoci hamsi aka kaiwa hari a kudancin kasar Sudan daga shekara ta 2016 zuwa 2017.

https://p.dw.com/p/2wXGZ
Südsudan UN denken über Verstärkung von Unmiss nach
Al'ummar kudancin kasar SudanHoto: Reuters/A. Ohanesian

Rahoton ya kara da cewar cikin hare-hare 750 da 'yan tawaye su ka kai a cikin kankanin lokaci, kayan agaji sun gaza kaiwa ga masu bukata sakamakon hana shige da fice yankunan da ke fama da rikicin da 'yan tawayen suka yi a kasar ta Cibiyar ta zargi bangaren gwamnatin da kuma na 'yan tawayen da konewa tare da sata da mamaye asibitoci da kuma tsare likitoci da ma'aikatan ayyukan agaji a matsayin dabarun yaki.