1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kudin bai daya a Afirka ta yamma

October 25, 2013

Kungiyar ECOWAS na sake duba batun samar da kudaden bai daya da kuma yin kasuwanci na bai daya, a kashen Afirka ta yamma domin bunkasa tattalin arzikin yankin.

https://p.dw.com/p/1A6Eo
Hoto: Reuters

Shugabannin kasashe 15 na yammacin Afirka dake cikin kungiyar bunkasa tattalin arzikin Afirka ta yamma wato ECOWAS, na gudanar da wani taro na musamman a Dakar babban birnin kasar Senigal, domin duba batun yin kasuwancin bai daya da kuma samar da kudaden bai daya a tsakanin kasashen nan da shekara ta 2020.

Taron wanda ake sa ran zaifi mayar da hankali kan batun tattalin arzki, zai kuma duba batun rikicin kasashen Mali da Guinea-Bissau da kuma fargabar da ake yi ta barkewar rikicin bayan zabe a kasar Guinea Konakri.

Da yake zantawa da manema labarai gabanin taron a birnin Dakar na kasar Senigal, shugaban kungiyar ta ECOWAS Kadre Desire Ouedraogo, ya ce suna so su mai da hankali kan batun tattalin arziki a wanna karon, ba kamar a lokutan baya ba da kungiyar ta saba zamowa kan gaba wajen sasanta rikici da kuma al'amuran siyasa.

Mawallafiya:Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita:Usman Shehu Usman