1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

KUDURIN MAJALISAR DINKIN DUNIYA KAN DARFUR, GAZAWA CE.

YAHAYA AHMEDJuly 30, 2004

Bayan doguwar tattaunawar da suka shafe kwanaki suna ta yi dai, mambobin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya sun yarje kan zartad da kuduri na bukatar Sudan ta dau matakan kawo karshen rikicin. A ganin REINHOLD MEYER, shugaban sashen Afirka da Gabas Ta Tsakiya na rediyo DEUTSCHE WELLE, wannan dai gazawa ce ta gamayyar kasa da kasa wajen warware rikice-rikice da ke kunno kai a duniya.

https://p.dw.com/p/Bvhd
`Yan gudun hijiran yankin Darfur, a kan hanyarsu zuwa Cadi.
`Yan gudun hijiran yankin Darfur, a kan hanyarsu zuwa Cadi.Hoto: AP

A doguwar tattaunar da suka yi ta yi kan rikicin nan na yankin Darfur, mambobin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, sun sake gazawa, wajen daukan sahihan matakai na kawo karshen addabar bil’adama da ake ta yi a wasu lokuta a sassa daban-daban na duniya. Duk wanda ya bi diddigin yadda tattaunawar ta kasance a Majalisar Dinkin Duniya, zai ga cewa, mambobin kwamitin sulhun sun rabu ne a rukunai daban-daban, inda kowa kuma ke yunkurin kare maslaharsa. A cikin wannan halin kuwa, da wuya a iya daukar tsauraran matakai na tilasa wa mahukuntan birnin Khartoum din yin katsalandan don kawo karshen addabar al’umman yankin Darfur da kungiyar Larabawan Janjaweed ke yi.

Kudurin da za a zartad a halin yanzu a kwamitin sulhun dai, ya bai wa gwamnatin Sudan din wa’adi ne na kwana 30, inda ta dau matakan tabbatar da tsaro da kare lafiyar jama’ar wannan yankin na Darfur. Bayan wannan wa’adin ya cika ne kwamitin zai sake zama kuma ya yi nazarin sakamakon da aka cim ma, da yanke shawara kan matakan da za a dauka nan gaba.

Babu shakka, kudurin ba zai haifad da wani sakamako na azo a gani ba. Saboda, yanzu ne bukatar daukar matakan gaggawa na ceto dimbin yawan rayuka a yankin na Darfur ta taso, ba a kwanaki 30 masu zuwa can gaba ba. Halin da ake ciki a yankin dai ya tabarbare ainun. Bai kamata ba kuwa, a ci gaba da bata lokaci kan yin dogon turanci kawai ba tare da aiwatad da wani mataki ba. Rikicin wannan yankin dai ya sanya wata alamar tambaya ne, kan yadda gamayyar kasa da kasa, ko ta kan kasashe dai-dai, ko kuma ta kan kafofin kasa da kasa, za ta iya samad da zaman lafiya da warware rikice-rikice a duniya. Ba za a iya dai amsa wannan tambayar ta yin la’akari da halin da ake ciki yanzu a yammacin Sudan ba. Abin da za a iya cewa a nan kawai shi ne, gamayyar kasa da kasa ta sake gazawa, wajen yin katsalandan don samad da zaman lafiya da warware rikice-rikice.

Wannan kudurin da za a zartar a Majalisar Dinkin Duniyar dai na nuna cewa, kwamitin sulhun ya yi asarar wata dama da ya samu, ta shiga tsakani don samad da zaman lafiya mai dorewa a yankin na yammacin Sudan. A daura da yayata matsalar da kafofin watsa labarai ke ta yi, mambobin kwamitin sulhun na kin bai wa wannan lamarin muhimmancin da ya cancanci samu ne, suna zaman oho ba ruwanmu, ko kuma suna yin watsi da yadda ababa ke wakana a yankin takamaimai.

Yayin da a cikin watannin baya-bayan nan, al’amura suka yi ta kara tabarbarewa a yankin Darfur, inda dubban jama’a suka rasa rayukansu, sa’annan aka kuma sami ambaliyar `yan gudun hijira, wadanda aka tilasa musu kaurace wa matsugunansu, babu wani sahihin matakin da gamayyar kasa da kasa ta dauka sai gudanad da taruka na dogon turanci kawai.

Annobar da ke aukuwa a Darfur dai na nuna cewa, dagewar da bangarori daban-daban ke yi wajen kare maslaharsu a huskar siyasa, da na tattalin arziki da na al’adu, ba tare da kula da yadda dimbin yawan rayuka ke salawanta a ko wace rana ta Aallah ba, su ne ummal aba’isin mafi yawan rikice-rikice da ake ta samu a duniya.

Wai shin, an manta ne da kisan kiyashin kasar Ruwanda? A galibi dai, sai aski ya zo gaban goshi kome ya kare dagulewa ne, za ka ga `yan siyasa sun fito suna ta dogon turanci, wanda kuma ko da wata matsalar ta kunno kai, ba za su dau matakin shawo kanta ba. Yayin da aka yi kisan kiyashin Rwanda dai, tsohon shugaban Amirka Bill Clinton da babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Kofi Annan, sun yi kira ga daukan matakan riga kafi na hana irin wannan annobar sake aukuwa.

To yanzu kuma, me ake jira wajen daukar matakan gaggawa na rage barnar da ke aukuwa a yankin Darfur? Ko dai har ila yau, gamayyar kasa da kasa ba ta koyi darasi ba ne daga annobar Rwanda da kuma rikicin Kwango?