1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar EU ta gargadi Iran kan yarjejeniyar nukiliya

Abdul-raheem Hassan
May 9, 2019

Kasashen Birtaniya da Faransa da Jamus sun gargadi Iran na yin watsi da yarjejeniyar nukiliya nan da kwanaki 60 idan EU ta gaza shawo kan matsalar takunkumin kasuwanci da kasar ke ciki.

https://p.dw.com/p/3IFmQ
Eröffnungsfeier Hannover Messe 2019
Hoto: picture-alliance/dpa/F. Gentsch

Kasashen Turai kawayen Iran da kungiyar EU sun jaddada aniyarsu ta cigaba da mutunta yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma da Iran a shekarar 2015. Sai dai a cewar Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, akwai bukatar a tinkari matsalar cikin hikima. "Ba ma fatan samun karin sabani, muna bukatar amfani da matakan diplomasiyya. Mun san iyakarmu, da zarar Turai ta cigaba da dunkulewa wuri guda. Kuma wannan shi ne matsayarmu. Samun kyakkyawar dama shi ne zai bamu ikon warware matsalar cikin sulhu."

Da ya ke ganawa da manema labaru a fadar White House na Amirka, Shugaba Donad Trump ya ce kofa a bude take ya tattauna kan rikicin kasuwanci tsakaninsa da Iran. Amma ya ce sai sun nuna bukatar haka da kansu.