1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar EU ta yi kira da a gudanar da zabe na adalci a Kongo

July 29, 2006
https://p.dw.com/p/Buol
KTT ta bi sahun MDD wajen yin kira ga al´umar kasar ta Kogo da su fita kwansu da kwarkwatansu wajen kada kuri´a a zaben na gobe lahadi. Wata sanarwar da kungiyar ta EU ta bayar ta nunar da cewa bayan shekaru fiye da 40 yanzu ´yan Kongon sun samu damar zabarwa kansu shugabanni ta hanyar demukiradiya. Kakakin rundunar EU a Kongo Peter Fuss ya ce sun kammala dukkan shirye shiryen kula da yadda zaben zai gudana. Sama da mutane miliyan 25 ake kwwautata zato zasu kada kuri´a a zabukan na shugaban kasa da na ´yan majalisun dokokin a Kongo.