Kungiyar IS ta aikata ta'asa a Siriya

An gano wasu manyan kaburbura guda bakwai na jam'i cike da gawrwarwaki mutane wadanda ba a tantance ba a kusa da garin Albu Kamal a gabashin Sirya tsohuwar tungar 'yan tawaye na kungiyar IS.

Hukumomi wanda suka ce gawarwakin sun kai 100 sun zargi kungiyar  IS  da laifin aikata ta'asar. Kungiyoyin kare haki bil Adama da na gaji sun ce yawancin wdanda suka mutu an gana musu hukuba ne kafin a kashesu. A cikin watan Nuwamba bara ne dai sojojin gwamnatin na Siriya suka sake karbar iko da garin na Albu Kamal da ga hannun kungiyar mayakan IS.

Bayanai masu kama

Rahotanni masu dangantaka