1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar IS ta ce ta kona dan Jordan da ta ke rike da shi

Muntaqa AhiwaFebruary 3, 2015

Kungiyar dake neman kafa daular musulunci IS, ta ce ta kashe matukin jirgi dan kasar Jordan da ta ke garkuwa da shi

https://p.dw.com/p/1EVA4
Jordanien - Pilot Maaz al-Kassasbeh
Hoto: picture-alliance/dpa/Jordan News Agency

Magoya bayan mayakan kungiyar IS mai fafutukar kafa daular musulunci, sun nuno wasu hotuna ta shafin Intanet dake nuna suna kona wani da ran sa wanda suka matukin jirgin saman nan ne dan kasar Jordan, Muath Al Kasaesbeh, wanda suke garkuwa da shi.

Koda yake ba a kaiga tabbatar da sahihancin fotunan na shafin Intanet din ba, mayakan na IS, sun nuno wani dake konewa ne a tsaye cikin wani bakin keji. Matukin jirgin na Jordan Muath Al Kasaesbeh dai, ya shiga hannun mayakan ne tun lokacin da jirgin da yake tukawa ya fadi a kusa da Raqqa na kasar Syria cikin watan Disamaban bara.

Kasar Jordan dai ta nuna aniyar amincewa mika wata 'yar Al Qaeda Sajida Al-Rishwa dake tsare a kasar, musayar da kungiyar ce ta bukace ta.