1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar IS ta ci kasa a birnin Rakka

Salissou Boukari
October 18, 2017

Kawancen Kurdawa da Larabawa da sojan da ke samun goyon bayan Amirka sun yi wa sojan IS taron dangi a birnin na Siriya inda suka tsere daga wuraren da suka ja daga.

https://p.dw.com/p/2m5Qs
Syrien Befreiung von Rakka
Hoto: Reuters/R. Said

Kungiyar 'yan jihadi ta IS ta rasa babban birninta a Siriya wato Rakka wanda a ranar Talata mayakan Kurdawa da na Larabawa da rundunar kawancen da Amirka ke jagoranta da marawa baya suka yi nasarar kwato birnin baki dayansa daga hannun 'yan jihadin bayan fafatawa ta tsawon watanni hudu. Tuni dai mayakan suka fantsama a titunan birnin inda suke nuna murnarsu ga wannan nasara da suka samu.

Kwace birnin Rakka da ke a matsayin cibiyar kungiyar ta IS a kasar Siriya, ba karamin koma baya ba ne ga 'yan kungiyar da suka yi ruwa suka yi tsaki a 'yan shekarun da suka gabata a kasashen na Siriya da ma Iraki inda suka mamaye manyan yankuna tun daga shekara ta 2014. Mayakan da Amirka ke marawa baya sun daga tuta a filin nan da ake kira Filin Rakka, da kuma filin Al-Naeem, da ke nuni da cewa a halin yanzu birnin da aka ragargaza ya fita daga karkashin ikon mayakan jihadin na kungiyar IS. Mai magana da yawun mayakan da suka kwaci birnin na Rakka Talal Sello, ya ce wannan fafatawa ce da aka yi gumurzu da mayakan sakan:

Syrien Befreiung von Rakka
A fata-fata da IS a Raqa har da dakaru mataHoto: Reuters/R. Said

" Rakka ya fada a karkashin kulawarmu yanzu haka. Amma dai wannan fafatawa ta kawo karshe, sai dai kuma abun  da zamu yi nan gaba shi ne bincikawa gida-gida domin ko zamu gano wasu ababe masu fashewa da suka bari, ko mu samu wasu mayakan na IS da suka buya."

Sai dai kuma  samun birnin na Rakka ya wakana ne yayin da yakin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 3,250 cikinsu fararan hula 1,130 kananan yara ma dai da suka mutu a kokarin kwato birnin na Rakka sun kai 270, yayin da adadin mayakan na bangarorin biyu  da suka mutu ya kai na mutane 2,120 a cewar kungiyar da ke sa ido kan kare hakkin bil-Adama ta kasar ta Siriya da ke da cibiya a birnin London.