1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kuri'ar nema wa siyasar Jamus mafita

January 21, 2018

Jam'iyyar SPD ta Jamus za ta kada kuri'ar bayyana matsaya kan yiwuwar a sami tattaunawa a hukumance da jam'iyyar CDU ta Angela Merkel a kokarin da ake yi na samun gwamnati tun bayan zaben kasa na watan Satumba.

https://p.dw.com/p/2rErP
Deutschland Außerordentlicher SPD-Parteitag in Bonn Martin Schulz
Martin Schulz, jagoran jam'iyyar SPD a JamusHoto: picture-alliance/dpa/K. Nietfeld

A wannan Lahadin ce jam'iyyar SPD a nan Jamus ke gudanar da taro domin yanke hukuncin karshe kan kulla kawance da jam'iyyar CDU ta Angela Merkel ko akasin haka. Taron wanda ke gudana a birnin Bonn ya karbi bakuncin 'ya'yan jam'iyyar da sauran masu fada a ji, inda a share guda wadanda ke adawa da yin kawance da CDU suka gudanar da zanga-zanga a gaban dakin taron.

Wakilai 600 na jam'iyyar SPD ne za su kada kuri'ar bayyana matsaya kan tattaunawa a hukumance da jam'iyyar CDU ta Angela Merkel. Baya ga su wadannan wakilan, akwai ma wasu 'yan jam'iyyar ta adawa SPD su dubu 440 da za su kada kuri'a ranar Lahadi a birnin Bonn.

Jagoran SPD Martin Schulz na fuskantar suka daga wasu daga rassan jam'iyyar musamman matasa, wadanda ke da ra'ayin jam'iyyar ta kafa kanta a matsayinta na mai adawa, saboda kayen da ta sha a zaben watan Satumbar bara.

Wasu jiga-jigan jam'iyyar ta SPD sun tabbatar da samun hadin kai a tsakanin 'ya'yan jam'iyyar da ke yanki mafi girma da kuma muhimmanci a siyasar Jamus, North Rhine-Westphalia, wadanda ke ra'ayin tattaunawar ta samu bisa sharadin jagoransu Martrin Schulz, ya jajirce kan manufofin da suka danganci shige-da-ficen baki da na lafiya da kuma wadanda suka shafi ayyuka.