1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kuri'ar 'yan kasar Iraki a ketare

January 18, 2005

'Yan kasar Iraki miliyan daya da rabi dake zaune a ketare ke da damar kada kuri'a a zaben kasar da za a gudanar a ranar 30 ga watan janairu

https://p.dw.com/p/Bvdc

Wannan dai shi ne karo na farko na farko da ‚yan kasar Iraki zasu kada kuri’a domin zaben wata sabuwar gwamnati da suke fata zata taimaka wajen kyautata makomarsu. An ji wannan bayani ne daga wasu ma’aurata daga kasar Irakin dake zaune a garin Essen, wadanda suka hallara a cibiyar zabe ta Kolon domin yin rajistar shiga zaben kasar da aka shirya gudanarwa a ranar 30 ga wata. To sai dai kuma duk da doki da murna da suke yi, suna kuma tattare da rashin sanin tabbas a game da ko shin ko da gaske za a gudanar da zaben tsakani da Allah kuma ko shin kome zai tafi salin-alin ba tare da fargaba ba. Domin kuwa ‚yan ta-kife sun yi barazanar kai hari akan duk wani dan kasar Iraki da yayi kurarin shiga wannan zabe. A sakamakon haka ma’auratan suka ki fadar sunayensu saboda tsoron makomar rayukansu. Ma’auratan tare da dansu guda daya su ne rukunin farko da suka hallara domin yin rajista a cibiyar zaben ta birnin Kolon. Kimanin jami’ai 80 aka tanadar domin sa ido akan zaben a cibiyar ta Kolon. A lokacin da yake bayani Khalil Zaweh, daya daga cikin jami’an sa idon ya ce kome na tafiya salin-alin ba tangarda kuma an dauki nagartattun matakai domin tsaron lafiyar masu shiga zaben. An tanadar da masu sa ido bakwai ga kowane rumfar zabe, saboda sa rai da ake yi na cewar kimanin Irakawa dubu 18 ne zasu kada kuri’unsu, bayan sun yi rajista a cibiyar ta Kolon. Gaba daya dai an tanadar da cibiyoyin rajistar masu zabe na kasar Irak kimanin 150 a kasashe dabam-dabam har 14 domin ba wa ‚yan kasa su kimanin miliyan daya da dubu 500 dake zaman hijira a ketare damar shiga a dama da su a siyasar kasarsu. A nan Jamus dai an tanadar da cibiyoyin zaben ne a biranen Kolon da Munich da Mannheim da Berlin. Amma dangane da cibiyar ta Kolon, hatta Irakawa dake zaune a kasashen Holland da Belgium, suna da ikon kada kuri’unsu a wannan cibiya. To sai dai kuma ma’auratan da suka hallara daga garin Essen domin rajista a cibiyar ta Kolon sun bayyana tababa a game da sakamakon zaben, inda shi kansa mai gidan yake cewar:

A hakika dai akwai rade-radin cewar tun da farkon fari aka shirya yadda sakamakon zaben zai kasance domin ba wa Allawi damar samun nasara. Ko da yake ban amince da gaskiyar wannan batu ba, amma ba shakka akwai wani surkullen da ake shiryawa a bayan fage. Na dai tabbatar da cewar Amurka ba zata yi kurarin yin katsalandan a sakamakon zaben ba ta la’akari da yawan jam’iyyun da zasu shiga takara.

A takaice dai zai dauki lokaci mai tsawo kafin Irakawa su farfado daga radadin da suka sha fama da shi karkashin mulkin Saddam Hussein da kuma yakin da aka kira wai na ‚yantar da Iraki, wanda har yau al’umar kasar ke sabani kansa.