1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwamitin sulhu zai kada kuri'ar neman sulhu a Aleppo

October 7, 2016

Faransa da Spain sun gabatar da kuduri da ke bukatar Rasha da Amurka su sulhunta rikicin Aleppo, don kawo karshen ruwan bama-bamai a kan fararen hula.

https://p.dw.com/p/2R1ho
Syrien Weißhelme
Hoto: Getty Images/AFP/T. Mohammed

A wannan Asabar din ce kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya zai kada kuri'ar neman amincewa da wannan kuduri.

Tuni dai Rasha ta nunar da manufarta na hawa kujerar naki dangane da kudurin da kasashen Faransa da Spain suka gabatar. Jakadan Rasha a MDD Vitaly Churkin ya ce, wannan ba kuduri ne da ya kamata a amince da shi ba, domin da gangan aka gabatar da dashi da nufin ingiza Rasha ta hau kujerar naki.

 "A kwai wasu abubuwa da za mu iya yi, akwai wadanda ba zamu yi ba, kamar shawagin jiragenmu. Amma ko shakka babu, kada su yi tsammanin cewar, za mu amince da bukatunsu, saboda kawai kwamitin sulhu ta bukaci hakan. Zan iya kada kuri'a ne kawai idan ya zo daidai da manufofinmu na soji".

Jakadan Faransa a zauren Francois Delattre ya sanar da gabatar da kudurin, domin wakilan kwamitin sulhun su kada kuri'un amincewa ko akasin haka a gobe Asabar, ganin cewar babu sauran lokacin batawa a kan rikicin na Aleppo.