1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwanaki 100 da hawan sabon firaministan Habasha

January 4, 2013

A lokacin da Hailemariam Desalegn ya hau kan kujerar firaminista an yi fatan samun kyakkyawan sauyi a wannan kasa mai al'ummomi daban daban.

https://p.dw.com/p/17ENP
Hoto: Getty Images

An yi wa Hailemariam Desalegn injiniya mai matsakaicin ra'ayi, wanda ya hau kan kujerar firaministan kasar Habasha wato Ethiopia a tsakiyar watan Satumban shekara ta 2012, bayan mutuwar Meles Zenawi, kallon mutumin da zai kawo sauyi a kasar ta Habasha. Da yawa daga cikin 'yan kasar sun yi fatan cewa nadin sabon firaministan zai bude kofar sabon yanayin siyasa da damar fadin albarkacin baki tare da kawo karshen tursasawa jama'a da kuma kofofin yada labaru.

Da farko dai an hango haske. Kwanaki kalilan gabanin rantsar da sabon firaministan, gwamnatin Habasha ta yi wa firsinonin siyasa kimanin dubu biyu afuwa daidai lokacin bukukuwan shiga sabuwar shekarar 'yan kasar ta Habasha. A lokaci daya kuma ta fara tattaunawa da kungiyar kwato 'yancin yankin Ogadan wadda a hukumance take matsayin kungiyar 'yan tarzoma. Yayin da sabon firaministan Hailemariam Desalegn ya nuna aniyar shiga sabuwar tattauna batun zaman lafiya da daddiyar abokiyar gabar kasarsa wato Eritrea, fatan da yawa daga cikin 'yan Habasha na samun kwanciyar hankali da wadata ya kusan tabbata.

Kwaskwarima maimakon sauyin manufa

Firaministan kuma injiniya mai shekaru 47 na da saukin lamari idan aka kwatanta da mutumin da ya gada wato Meles Zenawi, wanda ya tafiyar da wani mulkin danniya tun bayan mummunan rikicin zaben shekakar 2005. Ya taba rike mukamin gwamnan lardi, da ministan harkokin waje da na mukaddashin firaminista, ya kasance babban aminin Meles Zenawi. Dan karamar kabilar Wolayta ne, kuma ya kasance kyakkyawan zabi musamman a tsakanin manyan kabilu dake da angizo a kasar. Jason Mosley masanin kasar Habasha ne a cibiyar nazarin harkokin kasa da kasa ta Chatham House dake birnin London.

Meles Zenawi Ministerpräsident Äthiopien
Marigayi Meles ZenawiHoto: AP

"Samun wani daga karamar kabila kamar Wolayta wadda bisa al'ada ba ta cikin bangaren masu mulki, kwakkwarar alama ce. Sai dai dole ne a gani a aikace."

Shi kuwa dan jam'iyar adawa ta All Ethiopia Unity Party, Wondemagegn Demeke cewa yayi.

"Nadin Hailemariam shi ne irinsa na farko a tarihin kasarmu, domin baya cikin kungiyoyin da suka yi gwagwarmayar kwato 'yanci. Mu dukanmu mu yi mamaki. Mun damu cewa za a soke tanadin da kundin tsarin mulki yayi. Ganin an dauki tsawon lokaci kafin nada ministan harkokin waje, hakan ya nuna cewa har yanzu gwamnatin kawance ce ke juya akalar mulki. Saboda haka muke baki cewa tun bayan nadinsa ba a samu sauyin manufa ba."

Har yanzu ba ta sake zane ba

Ga kasashen dake ba wa Habasha taimakon raya kasa ma dokin da aka yi da farko ya gushe.

Da wuya a wuni ba tare da 'yan diplomasiyan yamma sun shaida shari'ar da ake wa 'yan jarida ba. Daga cikin 'yan jarida 11 masu zaman kansu da aka yanke wa hukunci karkashin dokar yaki da ta'addanci, har izuwa karshen shekarar 2012, guda shida na tsare ciki har da Eskinder Nega wanda ya samu lambar yabo na masu rubuce rubuce a shafin sadarwa na Blog. Tun wasum makonni Musulmi a kasar ta Habasha ke gudanar da zanga zanga a kowace ranar Juma'a don yin Allah wadai da tuhumar ta'addancin da ake wa wasu Musulmi 29 da suka hada da 'yan jarida da limamai da masu fafatuka.

Regierungspartei bei Wahlen in Äthiopien vorn
Habasha na da nakasu a manufar fadin albarkacin bakiHoto: picture alliance/dpa

A karshen shekarar 2012 wasu 'yan majaliar Turai 16 sun rubuta wata budaddiyar wasika ga firaminista Hailemariam inda suka yi kira gare shi da ya girmama 'yancin fadin albarkacin baki. Alexander Graf Lambsdorff na daga cikin marubuta wasikar.

"Sabon firaministan na da damar ciyar da kasarsa gaba idan ya tafiyar da gwamnatin da ta hada dukkan 'yan kasa. Ya ba da damar bayyana ra'ayi da kyautata dangantaka da kasashe makwabta musamman kasar Eritrea."

Idan firaministan ya yi haka to shakka babu zai aike da wani muhimmin sako da zai daga matsayin kasar ta Habasha a idon duniya.

Mawallafa: Ludger Schadomsky / Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu