1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabbin alkawuran Amirka wa Afirka

Philipp Sandner MNA
April 29, 2021

Bayan katobara da jahiltar nahiyar Afirka da tsohon shugaban Amirka Donald Trump ya yi, yanzu Amirka karkashin Shugaba Joe Biden ta koma bin manufofinta kan Afirka.

https://p.dw.com/p/3skAL
TABLEAU | 100 Tage Biden
Hoto: Melina Mara/Pool/Getty Images/AFP

Ga 'yan Afirka da dama dangantaka tsakanin Amirka da Afirka ta yi mummunan rauni a zamanin Shugaba Donald Trump. Da ma 'yan Afirka na korafin cewa Amirka muradun take bi kuma da zarar bukata ta biya sai ta juya wa Afirka baya. Trump a zamanin shugabancinsa bai nuna sha'awa ga Afirka inda ma ya yi ta kalaman na batanci ga nahiyar. Dan kasar Kamaru Achille Mbembe, sanannen mai kishin nahiyar Afirka ne, a cikin watan Numaban 2020, ya kwatanta manufar Trump game da Afirka kamar haka:

"Ina cewa Trump ba shi da wata sha'awar Afirka. Gaskiya a gare shi Afirka na zama wani nauyi ne. In ma ya nuna sha'awa ga nahiyar to a kan batun yaki da watakila 'yan ta'adda ne."

TABLEAU | 100 Tage Biden
Majalisar wakilan AmirkaHoto: Doug Mills/Pool/Getty Images

Waiwaye na watannin farko na gwamnatin Joe Biden ya samu yabo daga manazarta da suka hango farfadowar kyawan dangantaku a cewar Christian von Soest na cibiyar nazarin harkokin siyasar Afirka ta GIGA.

"Gwammatin Biden ta nuna sha'awar kyautata huldar dangantaka da Afirka har ma an fara gani a kasa, kamar yadda sabuar gwamnatin ta dage takunkumin shiga Amirka ga al'ummomin wasu kasashen Musulmi ko na Afirka. A gani na wannan gagarumin sauyi ne da ya nuna nan-take sauyin manufar gwamnati ga nahiyar Afirka."

Karin bayani: Amirka: Biden zai kara wa attajirai haraji

A cikin watan Maris sakataren harkokin wajen Amirka Anthony Blinken ya nuna sha'awar nada jakada na musamman ga yankin Kahon Afirka, bayan da farko sabuwar gwamnatin Amirka ta nuna rashi jin dadinta ga rikicin yankin Tigray na kasar Habasha, abin da ba aka rasa a lokacin Trump. Sai dai Christian von Soest na cibiyar GIGA ya ce manufar Amirka game da nahiyar Afirka na cikin tsaka mai wuya duba da halin da ake cikia Habasha. A hannu daya Habasha na zama babbar kawar Amirka wajen wanzar da zaman lafiya a yankin Kahon Afirka, amma a daya hannu sabuwar gwamnatin Amirka na ganin rikicin Tigray na barazana ga zaman lafiyar yankin.

Ba a dai sani ba ko Biden zai yarda da janye sojojin Amirka daga kasar Somaliya kamar yadda Trump ya ba da umarni jim kadan gabanin faduwarsa a zabe. A tsakiyar watan Afrilu ya jaddada matakin Trump na janye dakarun Amirka daga Afghanistan, a lokaci daya yana mayar da hankali kan barazanar ayyukan ta'addanci a fadin duniya.

TABLEAU | 100 Tage Biden
Kamala Harris da Nancy Pelosi da D-CalifHoto: Caroline Brehman/Getty Images

"Na ba wa jami'ai na umarnin sake fasalta dubarun tsaron cikin gida don sa ido su kuma katse duk wata barazana ta ta'addanci, ba a Afghanistan kadai ba, amma a duk inda za su kunno kai, akwai su a Afirka da Turai da Gabas ta Tsakiya a ko-ina akwai su."

Karin bayani: Biden ya sanar da dawo da tallafin Falasdinawa

Ko da yake batun yaki da ta'adda a Afirka na da matukar muhammanci, amma masana irin su Vanda Felbab-Brown ta cibiyar Brookings mai nazarin siyasar duniya, na gani ya kamata a hada da ayyukan raya kasa da samar ababan more rayuwa da karfafa matakan girka gwamnatoci na gari a Afirka da yaki da cin hanci da rashawa.