1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwango: Tshisekedi ya zama shugaban kasa

Zainab Mohammed Abubakar
January 20, 2019

Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ta fada cikin wani wadi na tsaka mai wuya a siyasance, bayan da kotun tsarin mulkin kasar ta tabbatar da Felix Tshisekedi a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa.

https://p.dw.com/p/3BrA9
Kongo, Kinshasa: Felix Tshisekedi, Vorsitzender der kongolesischen Oppositionspartei der Union
Hoto: Reuters/O. Acland

 

Alkalin kotun tsarin mulkin kasar Luamba Benoit ya ayyana sakamakon:

"Da gagarumin rinjaye, jama'a sun zabi Mr Tshisekedi Tshilombo Felix a matasayin sabon shugaban Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango"

Sai dai gabatar da wannan sanarwa ke da wuya, abokin takararsa wanda kuma ke binsa da mafin yawan kuri'u Martin Fayulu, shi ma ya ayyana kansa a matsayin zababben shugaba na zahiri da jama'a suka zaba.

Magoya bayan Fayulu na zargin hadin baki tsakanin Felix Tshisekedi da Shugaba Joseph Kabila mai barin gado, na yin arangizon kuri'u, bayan gaza tabuka komai a bangaren dan takara na jam'iyyar mai mulki.