1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotun Kwango za ta soma bincike kan zargin magudi a zabe

Ramatu Garba Baba
January 14, 2019

Daga ranar Talata, kotu a Jamhuriyyar Dimukuradiyyar Kwango za ta soma sauraron koken da aka shigar a gabanta kan zargin tafka magudi a zaben shugaban kasar da ya bai wa jagoran adawa Felix Tshisekedi nasara.

https://p.dw.com/p/3BXTP
Kongo, Kinshasa: Wahlen im Kongo
Hoto: Getty Images/AFP/T. Karumba

 

Dan takarar da ya zo na biyu,  Martin Fayulu, shi ya shigar da kara inda ya kalubalanci sakamakon zaben na karshen watan Disamba. Kotu na da tsawon mako guda da za ta yi nazari kan batun kafin ta iya zartas da hukuncinta.

An dai tsayar da ranar ashirin da biyu ga wannan watan na Janairu da muke ciki, a matsayin ranar da za a rantsar da sabon shugaban kasa kamar yadda hukumar zaben CENI ta sanar.

Yanzu haka jama'a na ci gaba da zama cikin fargaba, ganin rudanin da kasar ta shiga tun bayan fitar da sakamakon zaben. A daya bangaren kuwa, wasu kasashen duniya sun nemi a sake kidayan kuri'un domin gamsar da jama'a.