Kwango ta ƙulla yarjejeniyar sulhu da M23
December 12, 2013Kwango ta rattaɓa hannu kan wata yarjejeniyar sulhu da Ƙungiyar ta M23. Mai magana da yawun gwamnatin Kwango Lambert Mende ya ce takardu uku aka sanya wa hannu a faɗar shugaban ƙasar Kenya da ke Nairobi, kuma daga cikin abubuwan da suka tanadar har da rusa ƙungiyar M23 a matsayin ƙungiyar da ke fafutuka da makamai, da kuma tuba daga amfani da ƙarfi wajen cimma burinsu.To sai dai Mr Mende ya ce ba kowa ne za a yi wa afuwa ba domin a shirye suke su hukunta duk wanda aka kama da tabka laifukan yaƙi bisa tanadin dokokin ƙasa da ƙasa.
A wani labarin kuma babban kwamandan dakarun wanzar da zaman lafiya a Kwango ya kira wani taron manema labarai domin yin gargaɗi ga ƙungiyar 'yan tawayen FDLR da ke ɓoye a cikin dazukan ƙasar, da su kwance ɗammararsu ko kuma a kwance musu da ƙarfi da yaji. Majalisar Ɗinkin Duniya wadda aka yi ta suka na tsawon shekaru da dama yanzu, bisa gazawarta wajen kawo ƙarshen wannan rikici, ta fara ƙoƙarin farfaɗo da ƙimarta a idon al'ummar ƙasa da ƙasa tun bayan da ta yi nasarar tasa ƙeyar 'yan ƙungiyar M23 waɗanda suka kutsa suka kuma mamaye waɗansu mahimman garuruwa a yankin gabashin Kwango daga farkon wannan shekara.
Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Abdourahamane Hassane