1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaman zullumi bayan zabe

Mohammad Nasiru Awal MNA
January 7, 2019

'Yan Kwango na ci gaban da jiran bayyana sakamakon zabe yayin da manyan 'yan takara ke ikirarin yin nasara a zaben.

https://p.dw.com/p/3B97K
Kongo Präsidentschaftswahl | Wahllokal in Kinshasa
Hoto: Imago/Zuma Press

Al'ummar kasar Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango a wannan Litinin suna ci gaba da jiran a bayyana sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar 30 ga watan Disamban 2018. Hakan na zuwa ne kwana guda bayan da hukumar zaben kasar mai zaman kanta wato CENI ta ce za ta jinkirta bayyana sakamakon zaben har sai ta kammala tattarar dukkan kuri'un da ta samu daga tashoshin zabe.

'Yan Kwango a Kinshasa babban birnin kasar sun ce suna dakon sakamakon zaben suna masu yin kira ga hukumar ta CENI da ta nuna lalle za ta iya yin abin da ta dau alkawarin yi.

Elo Augustin wani direban tasi ne a birnin na Kinshasa da ya ce yanzu ana cikin zaman zullumi saboda rashin bayyana sakamakon zaben.

"Mun damu domin kamar yadda kuke gani yara ba sa iya zuwa makaranta saboda rashin sanin tabbas ko za a samu tashin hankali. Yara ba sa iya zuwa neman ilimi, su ne kuwa makomar Kwango ke hannunsu. Dole CENI ta bayyana sakamakon zaben da wuri don 'yan Kwango su iya fita zuwa aiki."