1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

"Mit Mut, Kreativität und Leidenschaft"

Usman ShehuAugust 15, 2013

A ƙasar Jamus an karrama wasu 'yan jaridan da suka yi fice wajen gudanar da ayyukansu, a ƙasashe daban-daban na nudiya.

https://p.dw.com/p/19QZ1
Auf dem Bild: Deutscher Medienpreis Entwicklungspolitik Preisverleihung am 14. August im Hauptstadtstudio Berlin. Fotos: Thomas Ecke / DW
'Yan jaridan da aka baiwa kyautaHoto: DW/T.Ecke

A ƙasar Jamus tun shekara ta 1975 aka ƙirƙiro da wata kyauta ta musamman ga 'yan jarida da suka yi banjita wajen aikinsu. 'Yan jaridan da ake baiwa wannan kyauta sun haɗa da wanda suka yi fice wajen aikin samar da ci-gaban ƙasa da kuma kare yancin ɗan Adam, a bana ma'aikatar raya ƙasashe ta Tarayyar Jamus da haɗin gwiwa tashar DW, suka bada kyautar.

Kyatar da aka baiwa 'yan jaridar dai, an bada ita ne ga nahiyoyi shida, nahiyar Afirka ta samu kyata ta musamman, wanda aka baiwa wasu 'yan jarida masu ɗaukar hoto.

Dalilin kyautar

Ministan raya ƙasashen Jamus Dirk Niebel, ya yi ƙarin haske kan mahimmanci, wannan kyautar da ake bayarwa, ga 'yan jaridan da suka bada gudumawarsu ga ci gaban al'umma. Wannan kuwa yana nufin mutanen da suka fito suka sadaukar da rayukansu, domin bayyana yancin faɗin albarkacin baki. Hakan dai yana nufin 'yan jaridan sun bada rahotonni kan al'amuran ci- gaba a ƙasashensu, musamman batun da ya shafi kare yancin ɗan Adam. A faɗar Dirk Niebel, wasu daga cikin yan jaridan, sun yi irin wadannan duk da wahalar da fadin albarkacin baki yake da shi, a ƙasashnsu, bisa matsin lamba daga hukumomi.

Auf dem Bild: Deutscher Medienpreis Entwicklungspolitik Preisverleihung am 14. August im Hauptstadtstudio Berlin. Dirk Niebel, Oluyinka Ezekiel Adeparusi (Preiträger Sonderpreis Fotografie) Fotos: Thomas Ecke / DW
Oluyinka Ezekiel Adeparusi, da Dirk NiebelHoto: DW/T.Ecke

Shi ma da yake jawabi, darakta janar na tashar DW Erik Bettermann, yace wannan kyautar za ta rufe bakunan maƙiyan faɗin albarkacin baki, kuma Bettermman yace kyautar alama ce da ta nuna cewa, duniya tana tare da 'yan jarida da ke sadaukar da rayuwarsu domin bayyana wa duniya halin da ake ciki, duk da irin wahalar da suke fiskanta a aikin nasu.

Auf dem Bild: Deutscher Medienpreis Entwicklungspolitik Preisverleihung am 14. August im Hauptstadtstudio Berlin. Fotos: Thomas Ecke / DW
Erik Bettermann, Darakta Janar na tashar DWHoto: DW/T.Ecke

Su waye aka baiwa kyautar

Kyautar da aka baiwa nahiyoyi shidda, yankin Latin Amirka an miƙa kyautar ga wasu 'yan jarida waɗanda suka ƙware wajen yin amfani da sadarwar zamani a ƙasar Kolombiya, wadanda aka bai wa kyautar sune Olga Lozano da Juanita Leon da kuma Marcela Pelaez. A Turai an baiwa Uwe H Martin ɗan ƙasar Jamus, wanda ya mayar da hankali na yin bincike kan ƙaruwar kafanonin gini-gini a duniya, inda kamfanonin ke ci gaba da karɓe filayen noma ana mai da su masana'antu.

'Yan jaridan da suka samu kyautar daga ƙasashen gabacin Turai da tsakiyar Asiya, an ya basu musu ne, bisa yaƙi da hukumoi masu hana yancin fadin albarkacin baki. 'Yan jaridan sune, Volha Malafeyechava daga ƙasar Belarus wanda ya maida hankali kan kare yancin masu auren jinsi ɗaya, abinda aka haramta a ƙasar. Sai Hanan Khandagji wanda ta mayar da hankali bisa rubuta labarin kare 'yancin naƙasassu da yara ƙanan da matasa, a ƙasarta wato Jordan.

In this Friday, Jan. 21, 2011 photo, children play during a short school break in the Makoko slum, in Lagos, Nigeria. Simple spelling lessons and multiplication tables still appear on the chalkboards in empty classrooms across Africa's most populous nation as officials take over the country's schools to conduct voter registration drives ahead of the April elections. But in the Makoko slum, where houses accessible only by canoe sit on stilts above the still and polluted waters of the Lagos lagoon, several schools for the poor remained open.(AP Photo/Sunday Alamba)
Rayuwa a anguwar Makoko dake LagosHoto: AP

'Yan Afirka da suka yi nasara

'Yan jarida da suka fi nisan ta kansu, wajen son rai a labarin da suke rubutawa, an bada kyautar ga Gunjan Sharma daga ƙasar Indiya, sai kuma Wade Williams ɗan ƙasar Laberiya. Shi kuwa ɗan Najeriya Oluyinka Ezekiel Adeparusi, ya samu kyauta bisa wani labarin da ya rubuta a kan anguwar talakawa, inda mai da hankali ga talakawan da ke zama a anguwar Makoko a birnin Lagos.

Mawallafa: Ralf Witzler/ Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu