1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yar Belarus ta lashe kyautar Nobel ta 2022

Usman Shehu Usman ZUD
October 7, 2022

'Yar kasar Belarus Ales Bialiatski da wasu kungiyoyin kare hakkin dan Adam na Rasha sun lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel ta 2022. Kwamitin Nobel da ke kasar Norway ne ya sanar da hakan a ranar Juma'a a birnin Oslo.

https://p.dw.com/p/4HumL
Yadda aka yi bikin bayar da kyautar Nobel a bana
Yadda aka yi bikin bayar da kyautar Nobel a banaHoto: Anders Wiklund/TT/picture alliance

Shugabar kwamitin bayar da kyautar ta Nobel din Berit Reiss-Andersen ta siffanta kyautar ta bana da wani mataki na girmama kudurin kare hakkin dan Adam, dimukuradiyya da fahimtar zaman lafiya a kasashe uku masu makwabtaka wato Belarus da Rasha da Ukraine.

Baya ga kyautar zaman lafiya akwai kuma kyautar Adabi wace Anders Olsson ya jagoranci bayar da ita. Ya yi karin bayani kan dalilansu na bai wa Bafaranshiya Annie Ernaux kyautar Adabin ta Nobel.

Bafaranshiya Annie Ernaux wacce ta lashe kyautar Adabi ta Nobel tare da mai kula da gasar
Bafaranshiya Annie Ernaux wacce ta lashe kyautar Adabi ta Nobel tare da mai kula da gasarHoto: Henrik Montgomery/TT News Agency/REUTERS

"Rubutun Annie Ernaux yana karkashin tsari mai tafiya da lokaci. Kuma hakan ya bayyana a cikin shekara ta 2008, a cikin littafinta na Turanci, mai suna 'The Years" in ji Olsson

An dai samu martani daga shugabanni kan wannan kyautar zaman lafiya da aka bayar, inda shugabar kungiyar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta jinjina wa "bajinta da jajircewar" masu fafutukar kare hakkin dan Adam a Ukraine da Rasha da Belarus. 

Wasu daga cikin 'yan fafutukar da suka lashe kyautar ta Nobel
Wasu daga cikin 'yan fafutukar da suka lashe kyautar ta NobelHoto: Efrem Lukatsky/AP Photo/picture alliance

Gwamnatin Jamus ta wallafa cewa "Wadanda suka lashe kyautar sun yi adawa da adawa, kuma sun yi yunkuri na yaki da zalunci a cikin kungiyoyin fararen hula kamar musamman yadda rayuwa take a Rasha da Belarus."