1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Labaran duniya

April 23, 2007

JDan takarar jam'iyyar PDP dake mulki a Nijeriya an ce shi ne ya lashe zaben kasar da aka gudanar a karshen mako

https://p.dw.com/p/Btvh
Zaben Nijeriya
Zaben NijeriyaHoto: AP

A halin da ake ciki yanzu gaggan ‚yan takarar zaben shugaban kasar Faransa guda biyu da suka rage Nicolas Sarkozy da Segolene Royal sun tashi haikan a kokarinsu na neman kuri’u daga magoya bayan Francois Bayrou, wanda bai kai labari ba, as zagaye na biyu na zaben da za a yi ranar 6 ga watan mayu mai kamawa. Dukkansu biyu na kokarin ganin sun samu goyan baya daga masu kada kuri’a kimanin miliyan shida da rara dake goyan bayan Francois Bayrou mai matsakaicin ra’ayin siyasa. A zagayen farko dai Sarkozy ya tashi ne da kashi 31 sannan ita kuma Royal ta lashe kashi 26 cikin dari na jumullar kuri’un da aka kada. A mayar da martani ga sakamakon zaben ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier ya bayyana damuwarsa a game da kashi goma cikin darin da dan takara Le Pen mai kyamar baki ya samu a zaben na kasar Faransa jiya lahadi.

Kwanaki biyu kacal bayan kammala zaben shugaban kasar Nijeriya da ya fuskanci tashe-tashen hankula da magudin kuri’u hukumar zabe ta kasar INEC ta ce dan takarar jam’iyyar PDP dake mulki, Umaru ‚Yar Aduwa shi ne ya lashe zaben. Bisa alkaluman da hukumar ta bayar ‚Yar Aduwa mai samun cikakken goyan baya daga shugaba mai barin gado Olusegun Obasanjo ya samu goyan bayan kuri’u miliyan 24 da dubu dari shida, a yayinda abokin takararsa tsofon janar na soja Muhammed Buhari ya samu goyan baya na kuri’u miliyan shida da dubu dari shida. ‚Yan hamayya dai sun yi Allah Waddai da zaben wanda suka ce ba a tafiyar da shi akan hanya ta demokradiyya ba. Masu sa ido na cikin gida sun nema da a soke sakamakon zaben. Kazalika su ma masu sa ido na kasashen Kungiyar Tarayyar turai sun yi kakkausan suka, suka kuma ce an kashe mutane sama da 200 a ‚yan kwanaki kalilan kafin zaben.

Mutane kimanin 50 suka mutu sakamakon hare-hare na kunar bakin wake a sassa daban-daban na kasar iraki. A garin Ramadi an kashe mutane 20 a yayinda aka halaka ‚yan sanda 10 a Bakuba. A can Mosul kuma wani bam da aka dana a cikin wata mota yayi bindiga ya kuma kasha mutane goma. Kazalika a Bagadaza wani dan kunar bakin wake ya kai hari a wani gidan cin abinci ya kuma kasha mutane shida. Rahotanni na mahukunta sun ce akalla mutane 89 suka ji rauni sakamakon wadannan hare-hare.

An fuskanci bata kashi tsakanin dakarun kungiyar kotunan musulmin Somaliya da sojojin kasar Habasha a fadar mulki ta Mogadishu. Wadanda suka gane wa idanuwansu abin dake faruwa sun ce sannan biyu sun yi amfani da bamabamai da gurnati. Akalla mutane 230 suka mutu sakamakon bata kashin da ake gwabzawa a Mogadishu tsawon kwanaki shida da suka wuce. A kuma halin da ake ciki yanzu kungiyoyin kare hakkin dan-Adam sun ce akalla mutane dubu 500 suka tsere daga birnin na Mogadishu.