1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Labarin Wasanni: 21.01.2019

Mouhamadou Awal Balarabe
January 21, 2019

Borussia Dortmund ta bi RB Leipzig har gida kuma ta doke ta da ci daya mai ban haushi. Ita ma Bayern Munich ba ta wahala ba wajen gasa wa Hoffenheim aya a hannu da ci uku da daya.

https://p.dw.com/p/3BucN
Fußball Bundesliga 18. Spieltag | RB Leipzig vs. Borussia Dortmund Witsel
Hoto: Getty Images/Bongarts/K. Hessland

Kungiyar Lobi Stars ta Makardin Najeriya ta yi abin fallasa a gasar zakarun kasashen Afirka. Kungiyoyin 16 da ke rike da kambun zakara na kasashen Afirka sun gudanar da wasa na biyu na rukunoni hudu da aka hada bayan wasannin share fage da na tankade da rairaya. Wannan dai shi ne karo na 23 da hukumar kwallon kafa ta kasashen Afirka CAF ke shirya gasar ta zakaru wato Champions Lig tun bayan kafa ta a 1964.

A rukunin farko kungiyar Lobi Stars ta Makurdin jihar Benue da ke wakiltar Najeriya ta sha kaye da ci nema da daya a karawa da ta yi da ASEC Mimosas ta Cote d' Ivoire. Ita kuwa Mamelodi Sundowns (Afs)- ta doke Wydad Casablanca (Mar) da – 2-1.

A rukuni na biyu kuwa, Espérance Tunis (Tunisia) da ke rike da kofin zakaraun Afirka ta lallasa -FC Platinium (Zimbabuwe) da ci– 2-0 . Ita kuwa Orlando Pirates ta (Afirka ta kudus)- ta samu nasara a kan Horoya ta (Guinea) – da 3- da nema.

Africa Cup of Nations Elfenbeinküste - Marokko
Dan wasan Cote d' Ivoire da na MarokoHoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Yayin da 'yan kwallon Nijar suka daura damarar tinkarar gasar 'yan kasa da shekaru 20 ta Afirka da kasarsu za ta dauki bakunci. Kwanaki 1 2 kenan suka rage a fara gudanar da gasar kwallon kasa ta 'yan kasa da shekaru 20 da haihauwa ta kasashen Afirka a Jamhuriyar Nijar. Duk da cewa kasar na fuskantar kalubalen tsaro a wani bangarenta, amma Nijar na son yi amfani da wannan dama wajen cusa kwallon kafa a zukantan 'yan kasar, kamar yadda kokawa ta kasance. Tuni ma hukumar kwallon kafa ta FENIFOOT da ma 'yan wasa na MENA National suka shirya tsaf don bai wa marada kunya a gasar da suke daukar bakunci.

A nan Jamus kuwa, ba a samu sauyi a teburin Bundesliga ba bayan da kungiyoyi 18 da ake da su suka gudanar da mako na 18 na kakar wasannin kwallon kafa na 2018 zuwa 2019. Borussia Dortmund ta bi RB Leipzig har gida kuma ta doke ta da ci daya mai ban haushi. Ita ma Bayern Munich ba ta wahala ba wajen gasa wa Hoffenheim aya a hannu da ci uku da daya.

Amma wasan da ya zo a hagunce shi ne wanda ya gudana tsakanin Bayer Leverkusen da Borussia Monchengladbach inda Gladbach ta yi wa Leverkusen ci daya mai ban haushi.

Australian 2. Runde Roger Federer Sieg gegen Evans
Hoto: picture-alliance/Zuma/CSM

A fagen Tennis, shahararen dan wasan nan dan asalin kasar Switzerland Roger Federer ya dibi kashinsa a hannu a wasan da ya yi da dan asalin Girka Stefanos Tsitsipas, da ci, 6-7 , 7-6 , 7-5, 7-6 , a jiya Lahadi a birnin Melbourne na Ostraliya. wannan dai shi ne karo na uku da Federer ya kasa tabuka abin kirki a manyan gasannin Tennis na duniya baya ga ta Wimbledon da us open. yanzu dai a matakin kusa da kusa da na karshen Tsitsipas da ke da matsayi na 15 a duniya zai yi wasansa na gaba ne da Roberto bautista ya yin da Frances Tiafoe zai kecec raini ne da rafael nadal