1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Labarin Wasanni: 29.10.18

Mouhamadou Awal Balarabe YB
October 29, 2018

Bayern Munich ta rage gibin da ke tsakaninta da Dortmund. Najeriya ta samu kanta a rukunin mutuwa a kwallon kafar bakin teku na kasashen Afirka da zai gudana a watan Disamba a Masar.

https://p.dw.com/p/37JOr
Fussball Bundesliga 9. Spieltag l Mainz 05 vs FC Bayern –  1:2 Torschuss
Hoto: Getty Images/Bongarts/A. Grimm

Tarayyar Najeriya ta san kasashen da za ta yi gogayya da su a fagen kwallon kafa na bakin teku da Hukumar kula da kwallon kafar Afirka (CAF) ta saba shiryawa bayan kowadanne shekaru biyu-biyu. A bikin hada jadawalin kasashe da ya guda a ranar Lahadi, kungiyar Soccer beach ta Najeriya da ta taba lashe gasar so biyu a Afirka ta samu kanta a rukuni na biyu wanda ya kunshi wadanda aka fi ji da su a Afirka, inda za ta kara da Senegal da ta kasance kasar da ta fi lashe gasar kwallon bakin teku a wannan nahiya. Sai kuma Libiya da Tanzaniya wacce za ta halarci gasar a karon farko. A daya rukunin kuwa, Masar za ta buga wasanninta ne da Côte d' Ivoire da Madagaska da ta taba lashe gasar so daya da kuma Moroko.

Birnin Sharm el Sheikh na kasar Masar ne zai dauki bakunci gasar kwallon kafa a bekun tekun daga tara zuwa 14 ga watan Disamban 2018.

A nan Jamus, Borussia Dortmund na ci gaba da kasancewa a saman teburin Bundesliga da maki 21 duk da tashi (2 da 2) da ta yi a gida a karawar da ta yi Hertha Berlin. Godiya ta tabbata ga Jadon Sancho wanda taurarinsa ke haskawa a Dortmund wanda ya ci duka kwallayen biyu. Sai dai bugun daga kai sai mai tsarin gida da Hertha Berlin ta ci gajiya a minti karshe na wasa ya bai wa Salomon Kalou farke kwallo da ake binsu.

Amma kungiyar da ta bada mamaki a wannan mako na tara na Bundesliga ita ce Bayer Leverkussen da ta bi Werder Bremen har gida kuma ta doke ta da (6-2). 

Großbritannien nach dem Hubschrauberabsturz in Leicester
Kungiyar Leicester na jimamin babban rashiHoto: picture-alliance/PA Wire/a. Chown

A wani labari maras dadi kuwa, attajirin kasar Thailand da ya mallaki kungiyar Leicester ta Ingila Vichai Sri-vad-dhana-pra-bha ya rigamu gidan gaskiya sakamakon hadarin jirgin sama da ya yi gabanin karawa da kungiyarsa ta yi da West Ham,

Jirgin sama mai saukar angulu da ke dauke da shi da wasu karin mutane hudu ya fadi ne jim kadan bayan da ya tashi daga filin wasa na King Power stadium. Tun a shekarar 2010 ne wanda ake yi wa lakabi da Khun Vic ne ya kara jari a kulub din Leicester, lamarin da ya sa ta lashe kambun zakaran Ingila a shekara ta 2016.

A daidai lokacin da Jamhuriyar Nijar ta tsaida Disamba a matsayin watan da za a gudanar da gasar kokawa ta kasa a jihar Tillabery, su kuwa 'ya'yan wannan kasa da ke da zama a Najeriya na kokarin yada wannan wasata hanyar shirya gasar sa da zumunci a kowane karshen mako a wurare da dama na kasar. Sanin kowane cewa 'yan kokawa 80 da suka fito daga jihohi takwas na Nijar za su fafata tsakaninsu da nufin lashe kyaututtuka ciki har da takobi. A kasashen waje kuwa 'yan Nijar na gudanar da kokawar ne don karfafa dankon zumuncin da ke tsakaninsu da masu masaukin bakinsu.