1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wasanni: Kalubalen kasashe a AFCON

Mouhamadou Awal Balarabe LMJ
January 3, 2022

Manchester city ta fara wasanta na farko a shekara ta 2022 a Premier League na Ingila da kafar dama, yayin da ta bare wa Real Madrid a la Liga na kasar Spain a gaban mitsitsiyar kungiya.

https://p.dw.com/p/455ws
Fussball - 2021 Africa Cup of Nations - Kamerun
Kamaru na shirin karbar bakuncin gasar cin kofin Afirka ta AFCONHoto: Alain Guy Suffo/empics/picture alliance

Wasu kasashe da za a dama da su a gasar cin kofin kasashen Afirka da Kamaru za ta karbi bakunci, na cin karo da matsaloli a fannin 'yan wasa ciki har da Senegal da Cote d Ivoire da Najeriya. Bayan da kasashe suka fitar da jerin sunayen 'yan wasan da za su buga gasar AFCON ko CAN din a Kamaru, wasu daga cikin tawagogin sun gamu da tsaiko a kan dalilai dabam-dabam ciki har da kamuwa da Covid-19 da kuma uwa uba samun dan wasan KCote d Ivoire Sylvain Gbohouo da laifin shan magani da ke kara kuzari. Wannan lamari dai ya yi matukar kada 'yan kwallon Cote d' Ivoire, wadanda a halin yanzu suke somun horo a kasar Saudiyya. FIFA dai ta dakatar da Sylvain Gbohouo mai tsaron gida na Les Elephants, saboda gwajin fitsari da aka yi masa a watan Nuwamba ya nuna cewa yana amfani da maganin kara kuzari. Sai dai Hukumar Kwallon Kafar Cote d' Ivoire ta daukaka kara tare da neman yin sabon gwaji. A halin yanzu, mai horas da 'yan wasa Patrice Beaumelle ya kira sabon mai tsaron gida Edan Ulrich N’Drin a matsayin wanda zai maye gurbin Gbahoua.#b#

Fußball | SSC Napoli | Victor Osimhen
Victor Osimhen ba zai iya bugawa Najeriya wasa a gasar AFCON ba saboda coronaHoto: Franco Romano/NurPhoto/picture alliance

A nata bangaren, Senegal na takun saka da kungiyar Watford kan kin sakin dan wasa Ismael Sarr. Tun a ranar 31 ga watan Disambar da ya gabata ne, kungiyar Watford ta Ingila ta sanar da Hukumar Kwallon Kafa ta Senegal cewa ba za ta saki Ismaël Sarr ba, wanda mai horas da 'yan wasa Aliou Cissé ya kira domin ya kare martarbar kasarsa a gasar AFCON. Sai dai Senegal da ta danganta wannan hali da "rashin mutumci" a cikin wata sanarwa ta ce ba za ta sabu ba, domin dole Watford ta amince da shawarar da dan wasan ya yaanke tare da mutumta dokokin kasa da kasa. Ita dai Watford ta ce Isamel Sarr na fama da rauni a gwiwa kuma yana bukatar lokacin domin murmurewa, amma Senegal ta sha alwanshi daukar duk matakan da suka dace domin samun biyan bukata. Ita ma dai Najeriya ba za ta dama dan wasanta Emmanuel Dennis da shi ma ke bugawa Watford ba, saboda ta sanar da gayyatar da ta yi wa matashin mai shekaru 24 a makare. Bisa ga a al'ada dai, ya kamata Najeriya ta tuntubi Watford kimanin kwanaki 15 kafin lokaci. Wannan dai koma baya ne ga Super Eagles, saboda zakakurin dan wasanta Victor Osimhen ya kamu da COVID-19, abin da ya sa shi ma ba zai iya fafatawa a gasar ta AFCON ba.

Niger Ringkamp
Issaka Issaka ya lashe takobin kokawar Nijar a karo na huduHoto: Gazali Abdou Tasawa/DW

Dan kokowar jihar Dosso Issaka Issaka ya lashe takobin gasar kokowar gargajiya ta kasa karo na 42, bayan da ya kayar da Aibo Hassan wani matashin dan kokowa na jihar Maradi. Wasan kokowar na karshe da ya gudana a birnin Yamai fadar gwamnatin Nijar, ya samu halartar baki daga ciki da wajen kasar musamman daga makwabciyar kasa Najeriya. Kuma abin ban sha'awar ma shi ne, shugaban kasa Mohammed bazoum da kansa ne ya mikawa gwanin kokawar Issaka da ke sanya da farar babbar riga da farin rawani kyautarsa ta takobi har da farin doki da aka tanada. Shi dai Issaka ya samu wannan nasara shekaru 41, bayan samun dan kokawa Yakouba Kantu na Maradi wanda ya lashe takobin kasa baki daya har sau uku a cikin tarihi. Wannan dai shi ne karo na hudu da Issaka daga jihar Dosso ya zama sarkin kokawar gargajiya na Nijar, bayan da ya lashe takobin.

Fußball Bundesliga | Borussia Dortmund - Eintracht Frankfurt | Tor: (1:0)
Akwai yiwuwar Erling Haaland ya bar kungiyar kwallon kafa ta Borussia DortmundHoto: imago images/ActionPictures

An bude kasuwar musayar 'yan wasan kwallon kafa ta lokacin hunturu a kasashen Turai, inda a daidai lokacin da ake jita-jita kan 'yan wasa tuni kasuwa ta yi halinta a game da wasu zakakurai a cikinsu. Jonathan Ikoné ya zama dan wasan Fiorentina a hukumance, bayan da kulob din Italiya ya sanar da zuwan dan wasan Lille na Faransa a kan kudi miliyan 15. Su kuwa jaridun Spain sun bayyana cewa, zuwan Kylian Mbappé a Real Madrid zai bai wa dan wasan alawus na Euro miliyan 40. Sai dai ana jin cewar kasuwar dan wasan za ta kaya ne a watan mayu. Dan wasan gaba na Borussia Dortmund dan Norway, Erling Braut Haaland mai shekara 21 ya tsegunta wa magoya bayansa cewa, zai taka tamaula a kasar Spain a kaka mai zuwa ba tare da bayya sunan kungiyar da zai koma ba. Barcelona na duba yiwuwar musayar Ousmane Dembele da dan wasan gaban Manchester United Anthony Martial. Kungiyoyin Manchester United da Manchester City da Chelsea na rububin sayen dan wasan tsakiyar West Ham Declan Rice. Kafin a rufe kasuwa, Newcastle na son sayen 'yan wasa shida da suka hada da Kieran Trippier na Atletico Madrid gabanin haduwarsu da Watford ranar 15 ga Janairu. Newcastle din ta kuma ta tuntubi Arsenal da ta ba ta aron Pierre-Emerick Aubameyang dan wasan gaba mai shekara 32 da ke fuskantar matsala da kocinsa Arteta. Kungiyar wadda ake kira da Magpies, na son biyan fam miliyan 50 domin dauko Darwin Nunez dan wasan gaban Benfica dan kasar Uruguay mai shekara 22.#b#

England Premier League-Spiel zwischen Manchester City und Everton Trophäe
Ko Manchester City na shirin sake lashe gasar Premier League a bana?Hoto: Michael Regan/Getty Images

A gasar Premier League din ta Ingila, Manchester City na ci gaba da cin karanta babu babbaka a saman teburi. City din ta samu nasara a kan Arsenal da ci biyu da daya, a wasan mako na 21 na Premier Lig. A yanzu dai tawagar mai horas da 'yan wasa Pep Guardiola na ci gaba da yi wa abokan hamayyarta zarra, inda maki 10 ke tsakaninta da Chelsea, wacce ta tashi biyu da biyu a wasan da ta yi da Liverpool wacce ta kasance a matsayi na uku. A nata bangaren, Arsenal na rasa ratar da ke tsakaninta da West Ham da Tottenham bayan da suka taka rawar gani a karshen mako, lamarin da ya sa suka fara yunkurin nausawa matsayi na hudu. Yayin da wasu lig-lig na kasashen Turai irin su Bundesliga ke ci gaba da hutun lokacin sanyi, wasunsu irin sun la Liga na kasar spain sun dora inda suka tsaya a farkon shekara ta 2022. Sai dai Real Madrid da ke saman teburi ba ta ji da dadi ba, domin ta sha kashi a hannun Getafe. Tun a ranar uku ga Oktoban bara ba a doke Real Madrid a la Liga ba, amma ta fadi kasa warwas a ranar Lahadi a gaban makwabciyarta Getafe da ci daya mai ban haushi, lamarin da ke zama abin mamaki saboda kungiyar na daga cikin kurayen baya da ke fafutukar ganin ba su gangara karamin lig ba. Sai dai duk da wannan rashin nasara, Real Madrid na ci gaba da rike matsayinta na jagora a Lig din kwallon kafar Spain. Sai dai Sevilla da ke biye mata baya a matsayi na biyu na wasa wukarta, domin kuwa tana wasannin cike gurbi biyu da ya kamata ta buga. Yayin da ita kuwa FC Barcelona ta fara shekarar 2022 da kafar dama bayan da ta doke Mallorca da ci daya mai ban haushi, nasarar da ta ba ta damar komawa matsayi na biyar.

Spanien Sevilla | La Liga | Pablo Martin Paez Gavira
Kakar La Liga ta bana ba ta zowa FC Barcelona da dadi baHoto: Joaquin Corchero/Spain DPPI/picture alliance

A Faransa, ba a buga gasar Ligue 1 a farkon wannan shekara ta 2022 ba, amma dai kamar yadda aka saba bisa al'ada wasannin neman lashe kofin kwallon kafa na kasar ne suka gudana. A karawar da aka yi tsakanin kungiyoyi biyu da ke buga babban lig, Montpellier ta lallasa Strasbourg da ci daya mai ban haushi. A wasa tsakanin manyan kungiyoyin Faransa kuwa, Bordeaux ta sha kashi a hannun Brest. Sannan daga cikin sauran kungiyoyin babban lig da suka fadi a gaban kananan kungiyoyi, akwai Clermont da Rennes. A gefe guda kuwa, laya ta yi wa Marseille da Saint-Etienne da Monaco kyan rufi, inda suka haye mataki na gaba na neman lashe kofin na Faransa. Paris Saint Germain, wacce yawancin 'yan wasanta suka kamu da Covid-19 ciki har da Lionel Messi za ta fafata da OC Vannes da ke wasa a lig na hudu na kasar.