1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamaru ta lashe gasar Afirka

February 7, 2017

Gasar cin kofin kwallon kafa na Afirka karo na 31 da Gabon ta dauki nauyi ya kawo karshe inda kasar Kamaru ta lashe kofin gasar na bana bayan da ta lallasa kasar Masar da ci biyu da daya.

https://p.dw.com/p/2X6eJ
Cameroon's Benjamin Moukandjo celebrates with the trophy and teammates after winning the African Cup of Nations
Hoto: REUTERS

Masu sharhi kan wasannin kwallon kafa da dama ne suka yi hasashen cewa kamar yadda ta kasance a shekara ta 1984 da kuma shekara ta 2008 inda Masar ta doke Kamaru a wasan karshe, ko a wannan karo ma tarihi ne zai maimaita kansa. Wannan fada ta ko kusa tabbata bayan da kafin zuwa hutun rabin lokaci dan wasan Masar Mohamed Elneny ya ci kwallo a ragar Kamaru. Sai dai tun daga wannan lokacin Kamaru ta karbe kwallo da sama da kashi 60 a cikin 100. Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci Kamaru ta yi sauyin 'yan wasa kana ta ci gaba da mallake kwallo, wanda haka ya kai ta ga barke kwallo a mintoci na 59 kafin saka ta karshe a mintoci na 88.kana ta rike daga har zuwa karshen wasan da aka tashi ci biyu da daya. Bayan kammala wasan dan wasan kasar ta Kamaru Arnaud Djoum ya bayyana gamsuwa:

African Cup of Nations Ägypten gegen Kamerun | Sieg Kamerun
Hoto: Reuters/A. Abdallah Dalsh

"Ya ce ina cike da farin ciki, kuma ina mai kyakutata zaton illihirin al'ummar Kamaru na ita ma cikin farin ciki. Domin abu ne  na alfahari da ban yi tsammani ba. Don haka na yi farin ciki sosai"

Shi ko mai horas da 'yan wasan kasar ta Kamaru Hugo Broos dan kasar Belgiyam magana ya mayar bisa wasu 'yan kasar ta Kamaru da suka jima suna sukar lamirinsa:

"Ya ce na yi farin ciki sosai da yin nasarar lashe kofin kwallon kafa na Afirka a yau, ina godiya da hadin kan da 'yan wasa suka bani cikin horauwar da na yi masu wajen dage wa ga aiki .Dama na sha fadawa 'yan jaridar kamaru masu sukar lamirin aikina cea su yi hakuri su ba mu damar kawo gyara a cikin wasanmu, komi zai je daidai zuwa gaba. ga shi a yau mun yi nasara.Ina fatan daga yanzu huldar mu da 'yan jaridar Kamaru zai ta ingantu"

Cameroon coach Hugo Broos celebrates with the trophy and teammates after winning the African Cup of Nations
Hoto: REUTERS

A biranen kasar ta Kamaru ma dai didima babu kama hannun yaro, jama'a sun kwan dare suna shagulgulla, kuma wasunsun sun bayyana gamsuwarsu da yadda a wannan karo suka yi nasarar karya caffin da ake yi wa Kamaru a gaban Masar:

"Ya ce ina cike da farin ciki domin shekaru kimanin 10 kenan da Kamaru ke shan kashi a gaban Masar a duk lokacin da suka hadu. Dan hada yau ina cike da farin cikin da alfaharin kasancewa dan Kamaru"

"Ita ko wannan cewa ta ke ina cike da farin ciki domin a karshe dai a yau  mun karya canfin nan da ke da akwai da ke cewa Kamaru ba za ta iya Nasara kan Masar ba. ga shi a yau mun doke su biyu da daya, wanda ke nufin zakunan Kamaru sun fi kowa karfi"

A yanzu dai Kamaru ta lashe kofin kwallon kafar na Afirka so biyar.

Afrika Cup - Finale - Kamerun - Ägypten  0:1 2008
Hoto: picture-alliance/dpa/T. Ridley

To sai dai a daidai lokacin da kasar Kamaru ta yi nasarar karya canfin da ake yi mata kan Masar daga na shi bangare mai horas da 'yan wasan kasar ta Masar Hector Cuper dan asalin kasar Argentina, kalular ta jima tana bin sa ce ta faduwar a dukkanin wasan karshe ko final da ya buga har yanzu bata rabu da shi.  A cikin shekaru 20 sau biyar yana shan kashi a wasan karshe a karkashin kungiyoyin da ya jagoranta a kasashen Spain da Italiya da Girka kafin a yanzu kuma tarihi ya maimaita kansa a kan kasar ta Masar: Kuma ya bayyana bakin cikinsa da faruwar hakan a wannan karo ma yana mai cewa:

"Ya ce na ji takaici da sake baras da wasan karshe, amma babban bakin cikina shi ne na kasa farantawa al'ummar Masar da ranta na cin wannan kofi wanda Allah ya sani sun hadamce masa sosai".

A kasar ta Masar dai dubunnan jama'a ne suka taru a gaban akwatinan talabijin domin kawallon wasan kuma da dama daga cikinsu sun bayyana takaicinsu da yadda sakamakon bai zo masu da dadi ba.

Da wannan nasar da ta samu Kamaru ta dauki kofin kwallon kafar na Afirka so biyar, amma Masar ce ke a sahun gaba da kofi bakwai, Ghana sau hudu, Najeriya tana da uku, Cote d'Ivoire da Jamhuriyar Demokaradiyar Kwango na da biyu biyu, sai kuma kasashen Zambiya, da Tunisiya, da Algeriya, da Sudan, da Afirka ta Kudu, da Maroko, da Habasha, da Kwango ko wannansu ya dauki kofi so daya.