Lafiya Jari: Me ke sa yara dolanta?

Mun duba cutar da ke shafar yara kanana da ke haddasa nakasa ta rashin ji ko gani ko kuma yaro ya kasance dolo a cikin yara 'yan uwansa.

Wannan cuta dai ta Sanfilippo a kan haifi yara da ita wadda kuma ake dangantawa da halita. Wani likita ne na Amirka dokta Sylvester Sanfilippo ya fara bincike a kanta a shekara ta 1963 mafarin ke nan da aka saka wa cutar sunan Sanfilippo.

Cutar wacce ta fi shafar yara masu misalin shekaru biyu zuwa uku tana da mataki dai-dai har zuwa uku. Wannan ciwo kan faru a dalilin gazawa ta yadda jikin dan Adam zai markada wasu sinadaran irin su glucose domin bin jini; sannan dadewa ko ci gaba da rashin aikin wasu sassan jikin na markade suga da aka sha ya kan iya janyo tabuwar kwakwalwa da hanta da kasusuwa da kuma hunhu.

Now live
mintuna 09:47
Duka rahotanni | 11.01.2019

Lafiya Jari: Me ke sa yara dolanta?

Har yanzu dai likitoci da kwararu ba su samu maganin wannan ciwo ba, amma a maganar da ake yi yanzu haka likitocin na gudanar da bincike domin yin gwaji kafin yin aure don gano cewar ko ma'auranta na dauke da kwayoyin cutar da ke iya janyo cutar Sanfilippo idan suka yi aure. Don jin cikakken shirin sai a latsa shirin da ke dauke da alama ta sauti.


Ƙarin rahotanni