1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Lalubo hanyar magance rikicin Ukraine

January 20, 2015

Shugabannin Turai na ci-gaba da duba hanyoyin da za'a magance fada tsakanin gwamnati da 'yan awaren Ukraine, inda fada ke kara rincabewa

https://p.dw.com/p/1ENTi
Ukraine Zerstörung in Donezk
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Nikolai

A gobe Laraba ne za'a gudanar da wani zaman taron tattaunawa a Berlin babban birnin kasar Jamus, kan karuwar rikici a gabashin Ukraine, inda wannan zama zai hada ministocin harkokin wajan kasashen Jamus, Faransa, Ukraine da kuma na Rasha. Da ya ke magana kan wannan batu, ministan harkokin wajan kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier, ya ce wannan haduwa da kasashen Rasha da Ukraine suka nemi a yi ta, za ta duba yiwuwar hana ci-gaban rikici da ke kara daukan wani sabon salo a gabashin kasar ta Ukraine.

Steinmeier ya kara da cewa, har yanzu akwai sabbin fadace-fadace masu tsoratarwa da ake fuskanta, tsakanin bangarorin a 'yan kwanakin baya-bayannan, inda ya ce ministan harkon wajan Rasha Serguei Lavrov, da takwaransa na Ukraine Pavlo Klimkin suka nemi shi da ya shirya wannan sabuwar haduwa. A wannan Talatar ma dai an ci gaba da gwabza fadan da manyan makammai a gabshin kasar ta Ukraine.

Mawallafi: Salissou Boukari

Edita: Usman Shehu Usman