1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yabo ga tsarin rajistar haihuwa ta SMS

Madelaine Meier/ ASSeptember 23, 2015

Al'ummar kauyen Songon na Ivory Coast sun yi maraba da tsarin yi wa jarirai rijistar haihuwa da wani matashi ya fito da shi don rage wahalhalun rayuwa saboda rashin shaidar takardar haihuwa.

https://p.dw.com/p/1Gbor
Videostill von BHAU150901_002_BirthRegister_01F
Hoto: DW

Rijistar yara ta haihuwa dai wani jan aiki ne ga mazauna kauyen Songon na kasar Ivory Coast domin kuwa sukan shafe tsawon lokaci kafin su kai ga inda za su samu a yi musu rijistar.

Wannnan kalubale da suke fuskanta dai ya sanya Jean Delmas kwararren mai amfani da na'urar kwamfiyuta kirkirar wani tsari mai suna Monihbah da za a yi amfani da shi wajen yin rijistar ta hanyar aikewa da sakon SMS.

Mr. Delmas ya ce tun da an samu tsarin sadarwa na zamani ya kyautu a ce an fiddawa mutanen wannan karkara kitse daga wuta dangane da wannan matsala, kuma ma a matsayinsa na uba da kuma shugaban al'umma yana ganin kamar hakki ne a kansa ya tallafa wajen warware wannan matsala.

Videostill von BHAU150901_002_BirthRegister_01F
Hoto: DW

"Mu kwararru ne na fasahar sadarwa ta zamani. Me ya sa ba za mu bada shawara ta yin amfani da hanyoyi masu sauki na yin rijistar yara don samun takardar haihuwa ba? Kamar yadda ku ka gani abin na da sauki. Na sha gaya wa kaina cewar dukanninmu iyaye ne a kauyukanmu don haka ya kamata mu taimaka."

Kalubale saboda rashin rajistar haihuwa

Yaran da ba su da rijistar haihuwa a Ivory Coast dai kan samu matsala wajen shiga makaranta ko samun takardar shaidar dan kasa ko ma yin zabe. Fitar da wannan sabon tsarin da Jean Delmas yayi da ma irin saukin da yake da shi sabanin wanda aka saba da shi da ke da wahalar gaske, ya sanya iyaye yin Allah san barka.

Aya Reine Koudio na daga cikin wanda suka amfana da wannan sabon tsarin na Jean Delmas.

"Wannan abu ne mai kyau garemu iyaye mata wanda ba mu da yadda za mu yi a yi wa yaranmu rijistar haihuwa."

Videostill von BHAU150901_002_BirthRegister_01F
Hoto: DW

Ita ma dai Nadege Kouma wadda ke yin aikatau a kauyen na Songon ta ce shirin na Jean Delmas ya rage musu wahalhalun da suke fuskanta wajen yi wa yara rijista musamman ma ga marasa karfi. Wannan ne ma ya sanya ta ce tun da 'yarta ta samu rijista yanzu kam za ta shiga makaranta don neman ilimi da zummar amfana wa kanta wani abu a rayuwa.

"Ina son 'yata ta yi karatu ta zama wata babba nan gaba. Ni ban yi karatu ba, shi ya sa ya zama dole ita ta yi don ta amfana wa kanta wani abu a rayuwa."

Fafatukar cigaba da sabon tsarin

DW dai ta zanta da Jean Delmas wanda ya samu lambobin yabo a kasashen duniya. Sai dai ya ce yana fuskantar koma baya sakamakon dakile shirin da gwamnati ke yi, sai dai ya ce hakan ba zai sa su gajiya ba.

"Za mu cigaba da shirin ba tare da mun karaya ba. Buri na shi ne mu kaddamar da tsarin na MôhNiBah ba wai a Ivory Coast kadai ba, har ma da Burkina Faso da Nijar da Togo da kuma Benin. Idan muka yi haka miliyoyin yara za su samu takardar shaidar haihuwa a hukumance."

Jean Delmas dai na cigaba da yin aiki tukuru don ganin dorewar wannan tsari nasa wanda a cikinsa yanzu haka jarirai 2000 suka samu rijista kuma tuni aiki ya yi nisa wajen karba musu takarda daga hukumomin kasar.