Lamuran siyasar Najeriya na daukan sabon salo
November 1, 2013Kasa da tsawon mako guda da hukuncin da ya haramta sabuwar PDP a cikin tarrayar Najeriya, hankula na tashe cikin gidan jam'iyyar, da ya zauna ya kalli kokarin sauyin sheka na 'yan bakwai daga gwamnoninsa da yanzu haka ke karbar bakuncin manyan shugabannin APC.
Sun dai fara da Sokoto kafin su kai ga Kano da Jigawa sanan kuma suka zarce Yola, fadar gwamnatin Jihar Adamawa. Duk dai da nufin aika sako ga uwar jam'iyar PDP da a baya ke tsallen murnar jana'izar sabuwar PDP, amma kuma ke fuskantar fatalwar da ke tada hankula cikin gidanta.
Babu dai zato ba kuma tsammani, 'ya'yan na sabuwar PDP da suka sha kaye a cikin kotu, suka kai ga sauyin takun tare da karkata zuwa ga adawa, abun kuma da ya haifar da wani sabon kawance da ziyarar 'yan bakwan a bangaren shugabannin jam'iyyar APC ta adawa. Abun da ya tada hankalin PDP, da ke kallon sabuwar rawar a matsayin kokari na yankan kauna, a cikin jam'iyyar da ta dauki lokaci ta na kokari na shawo kan matsalar, amma kuma ke neman kallon ficewar 'yan bakwan zuwa ga adawa.
Barrister Abdullahi Jalo dai na zaman mataimakin kakakin PDP da kuma ya ce, su har yanzu suna da sauran imanin hana gwamnonin barin jam'iyyar.
Kokari na shawo kai ga 'yan uwa, ko kuma rawar maita da abokai na hammaya dai, da alamu iyayen PDP na da jan aiki a kokarin sake mayar da tsinkakkun shanun zuwa garke, shanun kuma da a cewar Murtala Hamman Yaro Nyako da ke cikin gwamnonin da suka karbi bakwanci na masu zawarcin APC goron gayya na jana'izar tsohuwar uwar dakin ce kadai ke zaman abun da suke jiran karba ya zuwa yanzu.
To sai dai kuma ya zuwa yaushe goron gayyatar jana'izar ke shirin kai wa ga hannun 'yan bakwai dai, ana kallon kai kawon 'yan APC a matsayin wani sabon kwadon siyasa a tsakanin 'yan gidan na PDP, da suka dade suna kiran sunan sulhu, amma kuma ke ci gaba da matsin lamba ga masu tawayen.
Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Usman Shehu Usman