1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Lauya mai ceton al'umma kyauta a Kano

Nasir Salisu Zango/USUMarch 2, 2016

Barista Audu Bulama Bukarti, ya kan karbi shari'ar marasa galihu kuma ya kammala ba tare da ya karbi kudi ba a duk shari'a da ta shafi keta hakkin dan adam

https://p.dw.com/p/1I5Vi
Nigeria Symbolbild Korruption
Hoto: picture alliance/NurPhoto

Audu Bulama Bukarti gogaggyen lauya ne dan asalin jihar Yobe, amma kuma wanda ya yi karatu kuma yake zaune a jihar Kano. An haife shi a ranar 1 ga watan Janairun shekarar 1984, a garin Gashua da ke jihar Yobe. Matashin lauyan ya fara aikin koyarwa a jihar Yobe bayan kammala karatun kwarewa a fannin malanta wato NCE, kafin daga bisani ya koma tsangayar koyan aikin lauya a jamiar Bayero da ke Kano.

Bayan kammalawa a shekarar 2011, Bukarti ya shiga aikin lauya gadan-gadan, in da yake tsayawa marasa galihu kyauta. Sunan Barista Audu Bulama Bukarti ya kara yin tambari, lokacin zanga-zangar yaki da karin man fetur da aka yi a shekarar 2011 a Nigeria, in da ya tsayawa wasu matasa da aka kama.

Audu Bulama Bukarti ya ci-gaba da aikin lauya, tare da fafutukar kare hakkin jama'a, har zuwa shekarar 2014 lokacin da ya sami aikin koyarwa a tsangayar koyar da aikin lauya na jamiar ta Bayero a Kano.

Koda yake bahaushe kan ce taura biyu bata taunuwa, amma ga Lauya Bukarti ya ce wannan zance da sakel, domin ya ci gaba da fafutukar taimakawa marasa galihu duk da aikin koyarwa da yake yi, har ma yake cewar samun koyarwar ya zama tamkar karin karfin gwiwa ne gare shi. Yana mai cewar koyarwa da fafutukar kare dan adam tamkar dan juma ne da dan jimmai.

Abdullahi Iguda Panshekara, daya ne daga cikin irin mutanen da suka mori aikin jin kai na Barista Audu Bulama Bukarti, lokacin da 'yan uwansu suka rasu a wani kamfanin jimar fata, yace tsayawar Bulama ce ta fitar musu da hakkinsu.

Shi kuwa Habu Ibrahim dan uwa ne ga wani matashi Muhammad wanda hannusa guda ya daste lokacin da yake aiki a wani kamfani a Kano, ya bayyana cewar yanzu haka suna kotu kuma Audu Bulama Bukarti ne ya tsaya musu, a kyauta ba dan haka ba basu da karfin daukar lauya.

Yanzu haka dai galibin al'ummar jihar Kano fata suke da addu'ar samun karin lauyoyi masu fafutuka irin ta Barista Audu Bulama Bukarti, wanda yanzu haka yake kara karatun digiri na biyu a jami'ar ta Bayero da ke Kano.

Nigeria Bayero Universität in Kano
Hoto: Aminu Abubakar/AFP/GettyImages