1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Lawya ne zai zama firaministan Bozize

January 15, 2013

kungiyar tawayen seleka ta yi na'am da Barista Nicolas Tiangaye wanda 'yan adawa suka zaba a matsayin sabon firaministan Afirka ta Tsakiya a gwamnatin hadin kan kasa.

https://p.dw.com/p/17KYL
Hoto: DW/Leclerc

'Yan tawayen Jamhuriyar Afirka ta tsakiya sun amince Barista Nicolas Tiangaye ya zama firaminista a gwamnatin hadin kan kasa da ake shirin kafawa. Shugaban 'yan tawayen Michel Djotodia ne ya bayyana wannan matsayin na kungiyar Seleka, bayan da ya gana da shugaban Kwango Brazaville Denis Sassou Nguesso a Brazaville. Da ma dai ana jiran amincewar 'yan tawaye da zabin 'yan adawa kafin a nada Tiangaye a matsayin sabon firaminista.

Bisa ga yarejejniyar zaman lafiya da aka cimma tsakanin gwamnati da kuma 'yan tawaye dai, shugaba François Bozizé ba shi da hurumin tube firaministan da ake shirin nadawa kafin karshen wa'adinsa na mulki. Tuni dai dai 'yan adawan Seleka suka fara neman a nada daya daga cikin shugabanninsu a matsayin ministan tsaro. Sai dai bangaren gwamnati ya nunar da cewar ba za a yi rabon mukaman ba matikar bangarorin da ke gaba da juna ba su zauna akan teburi guda domin bazawa a faifai ba.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Usman Shehu Usman