1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kiran wayar neman bayanai a Nijar

Abdoulaye Mammane Amadou/ YBJuly 30, 2015

A Nijer dubban jama’a ne ke kira akan lamba 14 da ake kira "Tsanwan Layi" da hukumomi suka kirkiro da zummar bai wa jama’a damar yin tambayoyi cikin sirri game da dinbin cututtuka.

https://p.dw.com/p/1G71f
Afrika Kenia Frau telefoniert in Nairobi
Matasa da kiran wayaHoto: AP

Jama'ar kan yi tambaya kan batutuwa wadanda suka shafi na zaman takewar iyali ko cutar SIDA da ma batun kayyade iyali a kasar. Matakin dai ya taimaka ainun wajan bai wa jama'a damar tattaunawa musamman ma matasa game da cututtukansu na yau da kullum wanda ba kasafai suke iya tattauanawa kai tsaye ba da wani ko kuwa zuwa likita.


A cibiyar karbar kiraye kiranyen Tsanwan Layi ne wanda a kalla kusan ko wane minti daya mutane fiye da biyar ke kira domin samun shawarwarin ma'aikatan da ke aiki a cibiyar dangance da wasu cututukan da ke damun su.


Cibiyar na kumshe ne da m'aikata 10, a gabansu na'urorin kwamfuta ne dauke da takardun da ke kumshe da bayanai wanda mafi yawa suke bai wa masu kira.

A Nijer dai wasu alkalumma na cewa sama da kashi 33.2 cikin dari daga cikin al'ummar kasar fiye da miliyan 15 na shakku ko nuna dari darin zuwa ganin likita akai akai duk ko da tsananin ciwo ko kamarin da cutar da ke addabar su ke yi masu a jiki.

Altes Telefon
wayar tarhoHoto: BilderBox


Tunanin kafa tsanwan layin da hukumomin kasar ta Nijer suka yi sun ce ya taimaka ainin wajen shanwo kan wasu matsalolin kunya da kyamar zuwa likita daga wasu mazauna birane da karkara galibinsu matasa samari da 'yan mata inda da yawa kan bukaci shawarwari game da cututuka irin na zamantakewar iyali cikinsu kuwa harda cutar Sida.


Malam sallaou Issoufou Shi ne madugun tsarin na Lingne verte ya na mai cewa.
"A Maradi da Agadez da Tahoua da Diffa da daukacin jihohin Nijer ana kiranmu". To ko wadane irin shawarwari suke tambaya ? "A kwai wadanda suke cewa suna da ciwo wasu kuwa neman kariya suke game da cutar Ebola musamman ma 'yan Tahoua da suke zuwa kasashen kamar Gini haka kuma mata na tambayarmu yadda ya kamata su tsaida haihuwa kamar matasan mata, haka suna neman wannan karin bayani "

To ko me ke bai wa jama'ar kwarin gwiwar bata lokacinsu wurin kira maimakon zuwa kai tsaye ganin likita mafi kusa da su? Ga abinda Sallaou Issoufou yake cewa.
" To don saboda suna ganin layi ne wanda akwai sirri a cikinshi don haka suna samun kwarin gwiwa su yi kira su fadi gaskiyar cutar da ke damunsu sai suce wane ga cutar da ke damuna yaya ne zan yi".

Indische Frau telefoniert
Waya cikin sirriHoto: AP