1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Lebanon zata zama dandali na biyu na rikicin Siriya

October 22, 2012

Al'ummar Lebanon suna ci gaba da nuna tsoron makomar kasarsu bayan tashin hankalin da ya biyo bayan kisan Janar Hasasan

https://p.dw.com/p/16UW8
Hoto: Reuters

 Kisan da aka yiwa Janaar Wissam al-Hassan, dan darikar Sunni ranar Jumma'a, nan da nan ya zama sanadin  tayar da rikici mai tsanani a kasar ta Lebanon, abin da ya sanya tsohon Pirayim minista Saad Hariri yayi kira ga gwamnatin ta Lebanon gaba daya tayi murabus, saboda ta kasa daukar matakin hana kashe babban jami'in na yan sanda ko kuma dakatar da tashe-tashen hankulan da suka biyo baya. A  birnin Tripoli dake arewacin kasar, inda nan ne yan darikar Sunni suka fi yawa,  kuma wurin da ya zama matattarar masu adawa da shugaban Siriya, Bashar al-Assad,  tashin hankalin ya kai ga mutuwar mutane da dama. A birnin Beirut an jiwa mutane  masu yawa rauni, lokacin dauki ba dadi tsakanin  matasa masu  tashin hankali da jami'an tsaro. Majiyoyi suna kyautata zaton cewar an kashe al Hassan ne saboda a watan Agusta, bayan bincike mai tsanani,  hukumar da yake jagoranta ta tsaron cikin gida, ta kama  wani tsohon minista  dake da dangantaka ta kurkusa da  shugaban Syria Bashar al-Assad. Al-Hassan ya kuma jagoranci bincike  game da mutuwar tsohon Pirayim ministan Lebanon, Rafik al-Hariri, wanda shima a shekara ta 2005 ya rasa ransa sakamakon bom da aka boye cikin mota, inda a sakamakon wannan bincike, aka zargi yan Hisbolah da dama da laifin kisan. Lokacin jana'izar al-Hassan, shugabanin Lebanon sun yi kira ga jami'an tsaro su gaggauta  gano wadanda suke ga alhakin kisan jami'in a kuma gurfana dasu gaban shari'a. Shugaban kasa,  Michel Suleiman  yace:

"Ina kira ga hukumomin shari'a a kasarmu, kada  wani abu ya basu tsoro, saboda al'ummar Lebanopn suna  bayansu. Ina kira ga jami'anm tsaro su tsaya sosai kan aiikin su, ina kuma kira ga yan siyasa da gwamnati kada su yi kokarin  boye duk wasu aiyukan na marasa son kasarmu da masu aikata manyan laifuka."

Jim kadan bayan jana'izar, Pirayim minista mai ci, Najib Mikati yayi  tayin murabus daga mukaminsa, amma  shugaban kasa Micchel Suleiman ya nemi ya ci gaba a mukamin, domin hana Lebanon ta tsunduma gaba daya cikin halin yakin basasa.

Libanon Beirut Beerdigung al Hassans
Jana'izar marigayi Wissam al-HassanHoto: Reuters

Halin  da ake ciki a kasar Siriya,  ya watsu  zuwa cikin kasar ta Lebanon, inda tuni Syria din take da ruwa da tsaki  game da    siyasa a cikin kasar.  A Tripoli mai tashar jiragen ruwa, magoya baya da masu adawa da shugabannin Siriya suna ci gaba da yaki da  junan su, yayin da mazauna sauran yankunan kasar suke kara baiyana tsoron  cewar  Lebanon zata  zama dandali na biyu na yakin Syria. Wani mutum dake baiyana rashin jin dadin sa a game da halin da Lebanon din take ciki yace:

"A Lebanon mun kai matsayin da tilas ne mu fadi cewar yanzu  wajibi ne a dauki matakan da suka dace, saboda tuni  muna ji, muna gani kasar mu  tana kara tsunduma cikin rudami. Sannu a hankali ana kwace mana yanci da hakkinmu. Kashe Janar  Wissam al-Hassan babban koma-baya ne a garemu."

Najib Mikati Premierminister Libanon UN
Pirayim ministan Najib MikatiHoto: AFP/Getty Images

Wani  masani kan al'amuran gabas tsakiya,  Hisham Khouri  yace kashe Wissam al-Hassan da aka yi bai zama abin mamaki ba, saboda wannan wani matakine dake nuna fadadar abin dake gudana a Siriya tsawon watanni goma sha tara.

Mawallafi: Umaru Aliyu
Edita: Halima Balaraba Abbas