1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Libiya shekaru biyar bayan Gaddafi

October 20, 2016

A wannan Alhamis din ce ake cika shekaru biyar da kisan tsohon shugaba Gaddafi, amma har yanzu kasar ba alamun samun zaman lafiya inda ake fafatawa tsakanin mayaka wajen neman iko ciki har da IS

https://p.dw.com/p/2RUQC
Flash-Galerie Bildergalerie Gesichter des Jahres 2011 International Jahresrückblick
Hoto: AP

Tun a farkon wannan makon ne jiragen yakin Amirka suka kai sama da hari 30 a kan yankuna mayakan 'yan ta'adda na IS a birnin Sirte. Hakan na faruwa ne a daidai lokacin da dakarun da ke marawa gwamnatin Libiya baya, suke kai samame daga kasa da nufin kwace gundumomin karshe da ke hannun mayaka masu kaifin kishin addinin.

Tsawon shekara guda da rabi kenan garin Sirte ya koma matsugunnin mayakan na IS. Duk da cewar a yanzu an yi nasarar kakkabe mafi yawa daga cikinsu a yankin. Sirte mai dauke da yawan mutane sama da dubu 130 na da muhimmanci a tarihin kasar ta Libiya, wanda kuma ke zama mahaifar tsohon shugaban kasar Muammar Gaddafi, wanda ya gamu da ajalinsa a kusa da garin adaidai lokacin da yake kokarin tserewa a ranar 20 ga watan Oktoba 2011. 

Idan shekaru biyar bayan kawar da mulkin Gaddafi, har yanzu jiragen yakin Amirka na ci gaba da shawagi da sunan yakar 'yan tarzoma, bisa dukkan alamu da sauran rina a kaba, dangane da dalilan da aka gabatar a Paris da Washington da London, wandanda suka jagoranci sojojin NATO suka afkawa kasar ta Libiya a wancan lokaci.

Kawo yanzu ba'a cimma zaman lafiya a kasar ta Libiya ya kasance abu mawuci. 'Yanci da walwala da demokradiyya da inganta harkokin kasuwanci da aka yi fatan samu lokacin hambarar da Gaddafi, ya zama mafarki ne kawai. A madadin haka kasar ta sake fadawa cikin wani wadi na tsaka mai wuya, acewar Mattia Toaldo na majalisar gudanarwar Tarayyar Turai da ke kula da harkokin waje.

Symbolbild Luftangriff Libyen
Hoto: picture-alliance/dpa

"Ya ce gaskiya ne rayuwar yau da kullum wa 'yan Libiya ya dada munana. Akwai karuwar sace mutane, karancin kudi, da dai makamantansu. Sanin kowa ne harin hadaka da aka kai a wancan lokacin kan Gaddafi, ba karamin hari ba ne, wanda kuma kasashen Hadaddiyar Daular Larabawa da Qatar da da Turkiya suka taka rawa a ciki".

Jamus a wancan lokaci dai ta kaurace wa kada kuri'a don amincewa da yin amfani da karfi kan sojojin marigaye Gaddafi, haka suma kasashen Rasha da China. Ministan harkokin wajen Jamus na lokacin Guido Westerwelle ya sha suka daga 'yan siyasa da kafofin yada labaru. Dr Rolf Mützenich dan majalisan kasar Jamus ne a jam'iyyar SPD, kuma mataimakin shugaban kwamitin kula da harkokin ketare na majalisar.

Ya ce" Ina ganin shekara ta 2011 na da amsoshin dukkan abubuwan da ke faruwa yau a kasar Libiya. Al'ummar kasar suma sun nemi hadewa cikin ma'amalar kasa da kasa. Suna zaton cewar shekara ta 2011, za ta kasance sauyi a rayuwarsu bisa la'akari da juyin-juya hali na kasashe Larabawa, su ma sun cimma gaci na samun 'yanci" 

Shugaba Barack Obama dai ya bayyana samamen na shekarata ta 2011 da kasancewar mummunan kuskure da gwamnatinsa ta taba tabkawa. A Birtaniya an zargi David Cameron da alhakin rashin cimma matsayar da ta dace a kan Libiya. Shi kuwa Nicolas Sarkozy ya ba da hujjojinsa na hambarar da gwamnatin Gaddafi. Yanzu haka dai kasashen Afirka ne ke jin radadin halin da Libiya ke ciki kamar yadda Mattia Toaldo ya yi karin haske..

"Tun daga shekara ta 2011 ne dai aka fara samun fadadar rigingimu daga cikin Libiya zuwa wasu kasashe. Rikicin kasar Mali ya samu asali ne daga irin makamai da aka yi ta fitarwa a kasar ta Libiya. Hakan ya jagoranci yaduwar rikici a yankin Sahel baki daya". 

A yanzu haka gwamnatin hadin kan kasa da ke da goyon bayan MDD na fafutukar samun madafan ikon a Tiripoli, sai dai majalisar dokokin kasar da ke gabashi kuma mai adawa ta ki amincewa da gwamnatin. Faduwar gwamnatin Gaddafi dai ya jagoranci sace makamai masu dimbin yawa, wadanda aka samu yadawa zuwa kasashe makwabta kamar Nijar da Mali da Tunisiya, hakan kuma ya ba wa 'yan ta'adda kamar na IS damar samun matsowa kusa da kofar shiga Turai.