1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Libya: Hari cikin Masallaci a Benghazi

Salissou Boukari
February 9, 2018

Wani harin bama-bamai da aka kai a wannan Juma'ar a cikin wani masallacin Juma'a na birnin Benghazi a kasar Libiya ya yi sanadiyyar mutuwar mutum daya yayin da wasu 62 suka samu raunuka.

https://p.dw.com/p/2sQBT
Libyen Kampf um Bengasi
Hoto: Reuters/E.O. Al-Fetori

Wasu daga cikin wadanda suka samu raunukan na cikin mawuyacin hali sakamakon hari da aka kai cikin wani masallaci, inda bama-bamai biyu suka tashi a farkon soma sallar Juma'a a masallacin Saad Ibn Abou Abada da ke tsakiyar birnin na Bengazi mai nisan km 1000 a Gabashin Tripoli babban birnin kasar. An dai dana bam din a cikin makara da ke ajiye cikin masallacin, yayin da bam din na biyu aka dana shi  a wurin ajiye takalma.