1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Lieberman ya yi murabus

December 14, 2012

Ministan harkokin wajen Isra'ila, Avigdor Liebermann ya sanar da yin murabus bisa rashin amincewa da aka yi da shi a baya-bayan nan.

https://p.dw.com/p/172r9
Israel's Prime Minister Benjamin Netanyahu (R) and Foreign Minister Avigdor Lieberman shake hands at a joint news conference in Jerusalem October 25, 2012. Netanyahu and his main coalition partner Lieberman announced their plan to merge their right-wing parties ahead of Israel's January 22 election, on Thursday. REUTERS/Ammar Awad (JERUSALEM - Tags: POLITICS)
Liebermann( ta hagu) da NetanyahuHoto: REUTERS

Lieberman mai shekaru 54 ya ce ko da yake bai aikata wani laifi ba, to amma zai sauka daga muƙaminsa na ministan harkokin waje da kuma na mataimakin Firaminista . A jiya Alhamis ma'aikatar shari'ar ƙasar ta Isra'ila ta ce za a gurfanar da shi a gaban kotu bisa laifin cin hanci a da kuma halasta kuɗin haram.Ana dai rashin sanin tabbas game da tasirin da hakan zai yi akan zaɓen majalisar dokoki da zai gudana a watan Janairu.

A watan Nuwamban da ya gabata ne dai, jam'iyyar Liebermann mai matsanancin ra'ayin jari hujja da jam'iyyar firaiminista Benjamin Netanyahu ta Likud suka ba ba da sanarwar ƙulla ƙawance a zaɓen na watan Janairu.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Yahouza Sadissou Madobi