1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fasinjoji suna cikin damuwa

Zainab Mohammed AbubakarSeptember 9, 2015

Yajin aikin da matuka jirgin sama na Lufhansa suka fara a wannan Talatar, ya gurgunta harkokin zirga-zirga na gajere da dogon zango.

https://p.dw.com/p/1GTQQ
Deutschland Streik der Lufthansa-Piloten
Hoto: Reuters/K. Pfaffenbach

Kamfanin jiragen sama na Jamus Lufthansa ya gaza tsayar da yajin aikin da matuka jiragen suka fara, wanda ya jagoranci soke jirage wajen 1,000 a wannan Larabar.

Tun a jiya Talata ne dai kungiyar matuka jiragen na Lufthansa ta kaddamar da yajin aiki, wanda ya gurgunta tafiye-tafiye, tare da gargadin cewar lamarin zai dada muni idan har bukatarsu bata biya ba. Mai magana da yawun kungiyar Markus Wahl, ya ce akwai yiwuwar ci gaba da yajin aikin har zuwa cikin makonni masu gabatowa.

Yajin aikin da ke zama na 13 irinsa cikin tsukin watanni 18, ya tilasta kamfanin na Lufthansa soke jirage masu tafiya gajeren zango 84 daga cikin 170 a jiya Talata, kana a yau an soke jirage wajen 1,000, da ke zama kashi biyu daga cikin uku na jiragen da ya kamata su tashi, ciki har da masu tafiya dogon zango 52.

Kungiyar matuka jiragen saman ta kai kamfanin kara saboda shirinsa na daina daukar sabbin matuka jirage, karkashin dokokin gata na kwadago a Jamus. Kotu a birnin Frankfurt dai ta yi watsi da karar da Lufthansa ya shigar na haramta yajin aikin.