1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ma’aikatan mai a tarayyar Najeriya za su yi yajin aiki.

August 31, 2006
https://p.dw.com/p/Bul2

Ƙungiyoyin ƙwadagon ma’aikatan man fetur a tarayyar Najeriya, sun ce za su yi yajin aiki na kwana 3, tun daga ran 13 ga watan Satumba saboda kisan wani takwaransu da aka yi a tashe-tashen hankullan da ke ta yaɗuwa a yankunan kudancin ƙasar. Da yake bayyana haka a birnin Lagos, Peter Esele, shugaban ƙungiyar ƙwadagon manyan ma’aikatan haƙo man fetur a Najeria ya ce, ƙungiyoyin sun yanke shawarar yin yajin aikin ne, bayan kashe Nelson Ujeya, wani takwaransu da sojoji suka yi, yayin da suka buɗe wa kwale-kwalen da yake ciki wuta, bayan an ceto shi daga garkuwar da aka yi da shi har tsawon makwanni 20. Rahotanni dai sun ce mutane 12 ne suka rasa rayukansu a wannan ɗaukin da sojojin suka yi.