1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ma´aikatar harkokin wajen Sudan ta yi na´am da wata wasikar gargadi da ta aikewa wasu kasashe

October 7, 2006
https://p.dw.com/p/Buh5
Ma´aikatar harkokin wajen Sudan ta nuna goyon bayanta ga wata wasika da aka aikewa kasashe dama a cikin wannan mako, wadda a ciki Sudan din ta gargade su da ka da su ba da karo karon soja ga wata rundunar da MDD ke niyar turawa Darfur. Daukacin kasashen gamaiyar kasa da kasa sun nuna bacin ransu ga wannan wasika, wadda suka ce wata barazana ce daga Sudan. Kakakin ma´aikatar harkokin wajen Ali Sadiq ya ce duk kasar da tura sojinta zuwa Sudan ba tare da amincewar gwamnati ba, to za´a dauke ta a matsayin abokiyar gaba. Sadiq ya jaddada cewar wasika ta kara karfafa matsayin gwamnatin Sudan ne game da girke dakarun MDD a lardin Darfur, wanda yaki ya daidaita.