1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaAsiya

Gabilin mabiya addinin Islama sun yi bikin karamar Sallah

Suleiman Babayo
May 13, 2021

A kasashe da sassa na duniya gabilin mabiya addinin Islama sun yi bikin karamar Sallah sakamakon kawo karshe azumin da Musulman suka yi.

https://p.dw.com/p/3tLWU
Bildergalerie Fastenbrechen Philippinen Manila Eid al-Fitr
Hoto: Eloisa Lopez /REUTERS

A wannan Alhamis gabilin mabiya addinin Islama sun gudanar da bikin Sallah bayan kammala azumin watan Ramada, inda a sassa daban-daban na duniya aka yi bikin karkashin matakan yaki da annobar cutar coronavirus. A kasar Indonesiya da ke gaban gaba wajen yawan Musulmai a duniya an gudanar da sallah a masallatai a yankunan da annobar coronavirus ba da fadada ba, yayin da ake rufe masallatai ba tare da yin sallah a yankun da cutar ta ta'azzara. Shekaru biyu ke nan a jere ana bikin sallah karkashin matakan yaki da wannan annoba.

A kasar Malesiya Firamnista Muhyiddin Yassin ya kafa dokar hana fita ta kasa baki daya kwana daya kafin bikin sallah wanda ke nuna babu ziyara tsakanin 'yan uwa da abokan arziki, saboda matakin neman hana yada cutar ta coronavirus.

A yankin Zirin Gaza na Falasdinawa da tsagerun kungiyar Hamaske fafatawa da Isra'ila mutane sun yi sallah a gida saboda kazancewar rikici.