1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mace-mace a wani hari a kasar Afghanistan

Salissou BoukariJuly 23, 2016

Akalla mutane 30 sun mutu yayin da wasu 160 suka samu raunuka sakamakon fashewar bama-bamai a daidai lokacin da 'yan Shi'a ke jerin gwanon lumana a Kaboul.

https://p.dw.com/p/1JUnY
Afghanistan Kabul Selbstmordattentat
Hoto: picture-alliance/AP Photo/R. Gul

Mai magana da yawun ofishin ministan kiwon lafiyar kasar ta Afghanistan Mohammad Ismail Kawoosi ya tabbatar da wannan labari, yayin da wani dan jarida mai daukan hoto, shi ma ya tabbatar da cewa da idanunsa ya ga gawarwakin mutane kwance, yayin da wasu ma suka fatattake.

Dubban mutane dai 'yan Shi'a na kabilar Hazara suka yi wannan jerin gwano na lumana a birnin Kabul na Afghanistan domin nuna adawarsu ga wani yunkurin gina wani layi na wutar lantarki mai karfin gaske da zai bi ta yankunansu a jihar Bamiyan ta tsakiya inda suka ce yin hakan tamkar nuna wariya ne.