1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mace ta zama jagorar jam'iyyu a Afirka

Uwais Abubakar Idris
August 25, 2017

A karon farko an zabi Dr. Ramatu Tijjani Aliyu a matsayin shugabar majalisar jam'iyyun siyasun kasashen Afirka bayan taron da aka gudanar a birnin Khartoum na kasar Sudan, taron da bayan wannan ya tabo batutuwa da dama.

https://p.dw.com/p/2iqrH
Deutschland Beschäftigungstherapie für afrikanische Frauen
Hoto: DW/A. B. Jalloh

Dr. Ramatu Tijjani Aliyu ce sabuwar shugaba wacce dama ita ce shugabar mata ta jamiyyar APC a Najeriya wadda aka zaba a Sudan.Taron kungiyar da ya mayar da hankali sosai a fannin shawo kan dumbin kalubalen da ke fuskantar kasashen Afirka da dama, a tsarin demokurdiyya ta kuma hanyar amfani da jam'iyyun siyasun nahiyar wadda ke zama sandar duka. Kama daga ayyukan ta'addanci da rashin ayyukan yi zuwa koma bayan tattalin arziki, inda a karon farko aka zabi mace a matsayin shugabar kungiyar watau Dr. Ramatu Tijjani Aliyu wacce dama it ace shugabar mata ta jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta bayyana abubuwan da suka sa a gaba.

Flash-Galerie 100 Jahre Internationaler Frauentag : Zwischen Protest und Feier
Hoto: AP

To sai dai batun koma bayan da mata ke fuskanta a fannin siyasa ya fi daukar hankalin shugabar da wannan ne karon farko da aka zabi mace bisa wannan mukami. Ga sauran mata dai na ganin matsaloli da suke fuskanta kusan lamari ke da alaka da al'adar mutane Afrika da sai an yi watsi da su za'a samu ci gaba. To sai dai ga Hajiya Ruqaiyya Sanin a ganin mata su ne matsaloli kansu a kan batun siyasa. Sannu a hankali ana samun mata sabbin jini da ke shiga fage kamar yadda Comrade Maryam Uba Ahmad shugabar dalibai mata ta Najeriya ta bayyana.