1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Macron na bukatar rage yawan yan majalisa

July 3, 2017

Shugaban Faransa Emmanuel Macron yace zai rage yawan yan majalisun dokoki na dattijai da kuma wakilai da kimanin kashi daya cikin kashi uku.

https://p.dw.com/p/2frL6
Frankreich Emmanuel Macron, Rede in Versailles
Hoto: Reuters/E. Feferberg

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya gabatar da manufofi da zai baiwa fifiko a mulkinsa wadanda suka hada da lamuran siyasa da tsaro da kuma diplomasiyya.

Ya baiyana jadawalin ne a hadakar zaman majalisun dokokin kasar na wakilai da kuma dattijai.

Shugaban ya bada shawarar rage yawan yan majalisun dokokin da kimanin kashi daya cikin uku, yana mai cewa hakan zai bada damar samun inganci a ayyukan majalisar.

Faransa dai na da yan majalisun dattijai 348 da na wakilai 577.

Shugaba Macron ya bada misali da kunar kasa a matsayin abin da zai hada kan kowa da kowa ba tare da la'akari da banbancin siyasa ko akida ba.

Ya yi gargadi da cewa akwai bukatar gudanar da sauye sauye domin kaucewa yanayin da Faransa za ta zama saniyar ware yana mai cewa wajibi ne a duba kasafin kudi da kuma rage dumbin bashin da ke kan gwamnati.

Haka kuma yace wajibi ne a kawar da fargabar ta'addanci ba tare da kaucewa al'adu da dabi'unsu na kasa ba.