1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Macron ya lashe zaben shugaban kasar Faransa

Ahmed Salisu
May 7, 2017

Emmanuel Macron ya samu nasarar lashe zagaye na biyu na zaben shugaban Faransa da kusan kashi 65 cikin 100 na kuri'un da aka kada.

https://p.dw.com/p/2cZPr
Präsidentschaftswahl in Frankreich Emmanuel Macron
Hoto: picture alliance / Christophe Ena/AP/dpa

Tuni dai Le Pen ta amince da shan kaye a wannan zabe bayan da ta yi wani takaitaccen jawabi ga magoya bayan ta inda a nan ne ma ta taya Macron murna dangane da wannan nasara da ya samu.Shugabannin kasashen duniya sun fara aikewan da sakonninsu na taya murna ga zababben shugaban kasar ta Faransa. Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce nasarar da Macron ya samu nasara ce ga Turai baki daya, yayin da shugaba Francois Hollande da ke shirin barin gado ya bugawa Macron din waya don taya shi murna.

Ita kuwa Firaministar Birtaniya Theresa May a na ta bangaren cewa ta na taya Macron murna kana ta na fatan yin aiki da shugaban na Faransa mai jiran gado da zarar ya sha rantsuwar kama aiki kan batutuwa da dama kasancewar Faransa babbar aminya ce ga Birtaniya.