Mafarin rayuwar dan Adam a Afirka

Kwarangwal Lucy wacce aka fi sani da suna Dinknesh tana da shekaru miliyan 3.5. Kuma kasusuwa ne na bil Adama. An ganota a shekara ta 1974 a kasar Habasha.

Lucy ita ce kwarangwal mafi dadewa kana cikakka na halittar dan Adam na farko da ba a taba samun irinta ba a karni na baya bayan nan. Lucy ta taimaka wajen sanin ci gaban tushen bil Adama.


A shekarun 1974 masu binciken kimiyya suka samu kasusuwan da ke da kama da na mutum cikin jejin Rift na kasar Habasha. Cikin murna masanan da kwararru suna yin biki suna sauraren wani kida na Lucy in the sky. Makidan Beatles suka raira wanan waka, sannan daga nan ne kuma kwarangwal din ta dauki wannan suna na Lucy.

Bayan makonni biyu na bincike cikin zafin rana tawagar masu bincike sun tono daruruwan kasusuwan Lucy, wacce ta zama kwarangwal mafi zama cikakka ta bil Adama na farko wanda ba a taba samun irinta ba kamar yadda wani masanin tarihi na halittu da tsirrai Berhane Asfaw ya bayyana.


''Kashi 40 cikin 100 na jikin Lucy yana yadda yake, za a iya gane ta bambanta da sauran halittu na wancan zamani. Lucy ta zama wata hanyar bincike ta farko ta yin nazarin ci gaban halittar dan Adam shekaru da dama.''

Now live
mintuna 01:20
Tushen Afirka | 23.01.2018

Dan Adam ya fara rayuwa a Afirka

Lamarin yana da daukar hankali game da irin yadda samun wadannan kayan tarihi shi ne irinsa mafi dadewa da aka samu. Masana sun saukaka abin ta yadda za a iya fahimtar tushe da ci gaban halittar dan Adam a cewar dokto Robert Blumen Schine jagoran cibiyar binciken halittu da tsirrai na Afirka ta Kudu.


''A zahiri wata halitta ce da abin da ya yi mata saura sune kai da hakora wadanda ke da muhimmanci a cikin aikin bincike don gane nau'in abinci da take ci da kuma girman kwakwarta, amma kuma da wasu sauran kasusuwan da ke nuna cewar tana tafiya ne bisa kafafunta.''


Lucy takan iya tafiya kamar dan Adam sai dai kuma tana da wasu irin alamomin iri daya da na biri, hannayenta sun lankwasu kuma sun fi kafafunta tsawo, abin da ya sa ake tunanin ta kwashe rayuwarta a hawan bishiya, tsawonta ya kai sama da mita daya. Gano wannan kwarangwal na Lucy tare da wasu kasusuwan, ya nuna cewa Afirka ce cibiyar bil Adama a cewar dokto Robert Blumen Schine.

"Duk alamonin gwaggwan birin da ake iya kamantasu da bil Adama sun bayyana ne a nahiyar Afirka, daga kwakwarya da tunani na dan Adam wasu abubuwa ne da suka bambanta, sai dai kuma wani ci gaban halitta hasalima a Afirka.''


'Yan Habasha da dama sun fi son su kira Lucy da sunan Dinknesh abin da ake nufi da abin mammaki. Saboda Lucy ita kadai take, ana kuma ajiye da ita ne a gidan ajiye kayan tarihi na kasar. Ba a fitar da ita sai akwai wani babban taron baje koli na musammun, sai dai a kan samu kwarangwal na „Platre“ da ake yi a wasu sassan duniya tamkar Lucy wanda ake ajiye da su a gidajen tarihi har ma ta intanet a kan iya samunsu.


Wannan bangare ne na shiri na musamman Tushen Afirka "African Roots", shirin hadin gwiwa tsakanin tashar DW da Gidauniyar Gerda Henkel.